Gidajen Burodi a Mali
Da zarar rana ta fito a Bamako, Mali, motocin bas da masu talla da kura ke cika tituna. Amma kafin nan, a lokacin da 'yan tsitrarun mutane ke dawowa daga masallaci inda suka yi sallar asuba, ana iya ganin babura dauke da burodi irin wanda da yawa daga cikin mutanen za su ci don samun kuzari a ranar.

Asalin hoton, Annie Risemberg
Mali na da ingantacciyar al'adar girke-girke, kuma 'yan Mali na cin abincinsu na gargajiya, amma burodin wanda ya samo asali daga Faransa- mai dan karfi daga waje da lallausan ciki- ya zama abincin gargajiya a nan.
Ana yin burodin da filawa da gishiri da ruwa da yis kuma shi ne burodin da aka fi samu a gidajen burodi a Bamako, duk da cewa ana yi masu kwalliya da hotunan wani nau'in burodi mai kanannado.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Asalin hoton, Annie Risemberg
'Yan Mali da yawa ba sa sayen burodi daga gidajen gasa burodin sai dai daga kananan shaguna.
Direbobin da ke rarraba burodin ga shaguna na fara aiki ne daga karfe 4 na asuba, su kuwa ma'aikatan gidajen burodin na fara nasu aikin kafin karfe hudu.
Su kan fara kwaba burodin ne da tsakar dare.
Ana sayar da burodi da yawa ga shaguna da gidajen abinci har ma da gidajen biki.
Manajan Buru Niouman, Youssef Sogoba, ya yi baynain cewa gidan burodin na sayen baburan da ke rarraba burodin kowace safiya, dauke da daruruwan burodi.
"Duk lokacin da yawan burodin da ka raba ya kai 50,000, babur din ya zama naka," a cewarsa.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Asalin hoton, Annie Risemberg
A cikin gidajen burodi, maza na tashi daga baccin rana da suka yi a kan tabarmi yayin da burodin ke kumbura, mataki na karshe kafin a sa burodin a cikin manya Injin gashi da kuma rarrabawa.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Asalin hoton, Annie Risemberg
Ana sayar da burodi guda mai tsawon mita 1 kan kudin sefa 250, kuma a kan gasa burodi 2,500 a rana.
Duk da cewa burodi ba abincin gargajiya bane a Mali, 'yan Mali da yawa na cin burodi da kwai don karin kumallo.

Asalin hoton, Annie Risemberg
Duka hotuna daga Annie Risemberg











