Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mun fasa kada kuri'unmu a zaben Najeriya'
Wasu 'yan kasuwa a Najeriya da suka tafi garuruwansu na asali domin yin zabe sun ce ba za su iya tsayawa har a gudanar da zabuka ranar 23 ga watan Fabrairu ba.
Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta sanar da dage zabukan kasar da mako daya ranar Juma'a da tsakar dare, awowi kadan kafin a bude rumfunan zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 16 ga watan Fabraitru zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
Ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni daga ranar biyu ga watan Maris zuwa ranar tara ga watan na Maris.
Lamarin ya bata ran 'yan kasar da ma masu sanya ido da suka je kasar daga kasashen waje.
Masana harkokin tattalin arziki sun ce dage zabukan ya sa kasar ta yi asarar sama da $1bn cikin kwana daya kacal.
A hirsarsu da BBC, wasu 'yan kasuwa da suka baro jihohin Legas da Kaduna inda suke kasuwanci zuwa jihar Kebbi, inda za su kada kuri'a, sun ce ba za su jira zuwa makon gobe ba.
Daya daga cikinsu, Ibrahim Alawa, wanda ya tafi jiharsa ta Kebbi daga Legas domin yin zabe, ya ce harkar zabe ta fita daga ransa.
"Na baro Legas, ni da iyalina, da zummar wannan zaben. Mun yi abincin da za mu tafi da shi rumfar zabe mma da safe mai gadinmu ya gaya mana an dage zabe.
"Ni yanzu harkar zabe ta fita daga raina. Don ka ga an daga shi zuwa makon gobe, kuma shirin da na yi na zuwa makon gobe ne. Ka ga yanzu a ce wani sati ya kara fadowa cikin al'amurana, to gaskiya an dagula min lissafi. Zan koma Legas domin na ci gaba da harkokina", in ji shi.
Shi ma Malam Halliru Aliyu, wani dan kasuwa dan asalin jihar Kebbi da ke zaune a Kaduna, ya ce zai hada kayansa ya koma inda yake kasuwanci.
"Ban ji dadin dage zabe nan ba saboda na bar dukkan uzurina na taho gida domin yin zabe sai ga shi a ranar da na zo, da niyyar idan na kada kuri'a zan koma ranar Lahadi, amma an dage zabe.
"A gaskiya ba zan iya jira ba tun da Allah ya ga uzurina, kuma ya ga niyyata. Sai dai na yi fatan alheri ga duk wanda Allah ya bai wa mulki. Allah ya zaba mana shugaba mai adalci".
Sai dai wasu da dama da suka yi irin wannan tafiya sun sha alwashin ci gaba da zama a wuraren da suka je har sai sun kada kuri'unsu.