Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda wasu jami'an zabe suka yi kwanan zaune
Wata ma'aikaciyar hukumar zabe (INEC) ke zaune tare da kayan zabe da za a kai su wata rumfar zabe a ofishinsu da ke birnin Port Harcourt da ke kudancin Najeriya. Lamarin ya auku ne ranar 15 ga Fabrairu 2019, ana kwana daya kafin zabukan shugaban kasa da ma 'yan majalisar kasar. An dai shirya cewa 'yan Najeriya za su kada kuri'unsu ranar 16 ga Fabrairun.