Me ya faru a yakin neman zaben Buhari da na Atiku? Hotunan Afirka a makon jiya

Mun zabo muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka da 'yan Afirka a wasu wuraren a makon jiya.

Soweto Gospel Choir pose with their award at the 61st annual Grammy awards at Microsoft Theater on 10 February 2019 in Los Angeles, California.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a birnin Los Angeles, mambobin kungiyar mawakan coci ta the Soweto Gospel Choir sun dauki hoto bayan sun lashe kyautar Grammy.
Malian singer Fatoumata Diawara performs onstage during the 61st annual Grammy awards pre-telecast show on 10 February 2019 in Los Angeles, California.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mawakiya 'yar kasar Mali Fatoumata Diawara ta cashe a ranar, a wurin bikin ba da lambar yabon ta Grammy inda aka sanya hotuna, ciki har da na dalar Masar.
People dance and sing next to Ugandan singer Jackie Akello (C) during the 16th International African music festival 'Sauti za Busara' at the Old Fort in Stone town, Zanzibar, on 8 February 2019.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a, mawakiya 'yar kasar Uganda Jackie Akello, sanye da tufafi masu launin ruwan goro, ta bi sahun sauran jama'a a wurin bikin the Sauti za Busara...
African musicians perform in front of a huge mural on stage at the 16th International African music festival 'Sauti za Busara' at the Old Fort in Stone town, Zanzibar, on 8 February 2019.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da bikin ne, wanda ake yi duk shekara, a Stone Town da ke yankin Zanzibar na kasar Tanzania...
People wait for a show to begin at the 16th International African music festival 'Sauti za Busara' at the Old Fort in Stone town, Zanzibar, on 8 February 2019.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan kallo sun je daga sassa daban-daban na Tanzania da kuma nahiyar Afirka domin su kashe kwarkwatar idanunsu.
A boy dances at Ribadu Square, Jimeta, Adamawa State, Nigeria where the opposition Peoples Democratic Party (PDP) is set to hold a rally, on February 14, 2019. Nigerians will cast ballots on February 16 in presidential and legislative elections.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan yaron yana yin rawa a wani wurin taro da ke jihar Adamawa ta Najeriya gabanin gangamin yakin neman zaben da jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party ta yi ranar Alhamis a wurin.
Ranar Talata, mutum 15 ne suka mutu sakamakon turmutsutsu da aka yi a wajen gangamin yakin neman zaben Shugaba Buhari na jam'iyyar APC a birnin Port Harcourt. An dauki wannan hoton kwana daya bayan faruwar wannan iftila'i

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Talata, mutum 15 ne suka mutu sakamakon turmutsutsu da aka yi a wajen gangamin yakin neman zaben Shugaba Buhari na jam'iyyar APC a birnin Port Harcourt. An dauki wannan hoton ne kwana daya bayan faruwar wannan iftila'i
A woman smiles as she holds Valentine's Day gifts in a shop in Lagos' main airport on 13 February 2019. Supermarkets and shops stockpiled with Valentine's Day flowers and cards across the country are recording low sales because people are preoccupied with upcoming elections due on 16 February,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar 16 ga watan Fabrairu aka so gudanar da zabuka a Najeriya. Wasu masu kantuna sun ce shirye-shiryen zabukan sun hana su yin ciniki sosai domin zagayowar ranar Masoya ta duniya inda ake sayen irin wadannan kayan da ake bai wa masoya kyautuka.
Packaged roses sit at Wildfire Flowers on 12 February 2019 in Naivasha, Kenya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An shirya wadannan furanni ne a Kenya ranar Talata domin kai su ga masu bikin zagayowar ranar Masoya ta Duniya...
A man packages hypericum flowers at Wildfire Flowers on 12 February 2019 in Naivasha, Kenya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kenya ce kasa ta uku da ke fitar da irin wadannan furanni zuwa kasashen duniya, a cewar wasu alkaluma daga ofishin kididdiga.
Ranar Lahadi, an kaddamar da mutum mutumin Sarkin Daular Habasha, Haile Selassie a hedikwatar Tarayyar Kasashen Afirka da ke birnin Addis Ababa na Ethiopia. Lokacin mulkinsa, ya taimaka wajen kafa Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Ranar Lahadi, an kaddamar da mutum mutumin Sarkin Daular Habasha, Haile Selassie a hedikwatar Tarayyar Kasashen Afirka da ke birnin Addis Ababa na Ethiopia. Lokacin mulkinsa, ya taimaka wajen kafa Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka.
Ranar Asabar, an nada Sabrine Khalifa Mansour a matsayin sarauniyar kyau ta Tunisia ta shekarar 2019 a bikin da aka yi a birnin Tunis.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Ranar Asabar, an nada Sabrine Khalifa Mansour a matsayin sarauniyar kyau ta Tunisia ta shekarar 2019 a bikin da aka yi a birnin Tunis.

An samu wadannan hotuna ne daga kamfanonin dillancin labaran AFP, Anadolu Agency da kuma Getty Images