Yadda maganin sauro ya kashe 'yan mata uku 'yan gida daya a Kano

Asalin hoton, Habeeb Ahmad
- Marubuci, Daga Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Kano
Mahaifinsu ne dai ya gano gawarsu.
Zakiyya mai shekara 17, da Walida mai shekara 16, da Wasila mai shekara 11 sun kwanta ne a cikin dakin da suka fesa maganin sauro kuma suka toshe ko'ina.
Zuwan mahaifinsu ke da wuya don ya tashe su don su yi shirin tafiya makaranta da safe, sai kawai ya tarar da gawarwakinsu.
Mai taimaka wa gwamnan Kano kan harkokin matasa Habeeb Ahmad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce 'yan matan sun rasu ne a ranar Lahadi.
Sai dai mahaifin nasu bai ce komai ba lokacin da sashen Pidgin na BBC ya yi yunkurin jin ta bakinsa.
Yadda maganin sauro ya jawo rasa rai
Habib Ahmad ya musanta cewa guba ce ta halaka 'yan matan.
"Mun kai su asibiti kuma likita ya tabbatar mana da cewa maganin sauro ne da suka yi amfani da shi ya haddasa rasuwarsu".

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar al'amarin, kuma ta ce maganin sauro ne silar rasuwar tasu.
Abdullahi Haruna na rundunar ya ce "gaskiya ne likitoci sun ce maganin sauro ne, amma za mu ci gaba bincike kuma za mu sanar da ku idan mun kammala".
Sauro ya addabi Kano
A kididdigar yawan al'umma da aka yi a shekarar 2006 a Najeriya Kano tana da yawan mutane miliyan 16.3, sannan kuma jihar ta fi kowacce fama da cutar zazzabin cizon sauro na malaria.
A yanzu haka dai akwai kamfanonin yin maganin sauron da yawa a jihar saboda girman matsalar.














