Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwana 11: Tasirin iyayen gidan siyasa a zaben Najeriya na 2019 #BBCNigeria2019
- Marubuci, Daga Mayeni Jones
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC News a Najeriya
"Iyayen gida" a Najeriya ba sa tsayawa takara da kansu, amma sun yi amannar cewa suna da tasiri sosai kan wanda zai yi nasara, ko rashin nasara a zabe.
Yayin da aka fara yakin neman zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, wadannan mutanen suna da tasiri kan wane ne zai samu nasara a zaben.
Suna daukar nauyin 'yan takara, inda suke amfani da tasirinsu da dukiyarsu wajen ganin cewa dan takarar da suke goyon baya ya kai ga gaci.
'Yan siyasan da suke samun goyon bayan wadannan manyan mutanen, suna zabo mutanen da za su mara wa baya ne ba don suna da wata kwarewa a siyasance ba.
Suna mara wa dan takara baya ne, idan suna da tabbacin cewa zai biya su a gaba.
Wannan alakar ita ake kira siyasar "uban-gida" ko Godfatherism a Turancin Inglishi, kamar yadda wani malamin kimiyyar siyasa a Jami'ar Legas Dokta Dele Ashiru ya bayyana.
"Ana maganar wata dangantaka inda wani sanannen mutum da yake da tasiri a siyasa zai mara wa wani baya, a matsayin dan takara lokacin zabe."
"Iyayen gidan za su iya bakin kokarinsu don ganin wanda suke goyon bayan ya ci zabe."
"Dole sai iyayen gidan sun kasance masu tasiri, kuma yawancinsu suna rike, ko sun taba rike wani mukamin siyasa," in ji malamin jami'ar.
Yadda siyasar uba gidan ke baci
A sauran sassan kasar, siyasar jihar Kano, jihar ta fi kowace Musulmi a kasar ta fi gaban ta uban-gida.
Jihar Kano ce ta biyu a yawan masu kada kuri'a wanda hakan dama ce ga manyan jam'iyyun APC da PDP domin samun nasara.
Ana ganin cewa jama'a na yi wa Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso biyayya ne sau-da-kafa saboda shirin bayar da ilimi kyauta da gwamnatinsa ta aiwatar.
Kuma duk dan takatrar da ya samu goyon bayansa to zai samu kuri'u masu yawa a Kano.
Har ma yana da wata kungiya ta siyasa mai suna Kwankwasiyya wadda ake iya gane biyanta ta hanyar shigarsu ta jar hula da fararen kaya.
Yana mara wa Abba Kabir Yusuf dan takarar jam'iyyar PDP baya, bayan da ya raba gari da tsohon abokin siyasarsa.
Hotunan Rabi'u Kwankwaso sun fi girma a jikin allunan talla sama da na dan takarar PDP din kansa.
"Duk gidan da ka shiga a Arewacin Najeriya za ka tarar da mabiya kwankwasiyya daga cikin 'ya'yan gidan, ko mai gidan, ko uwar gidan ko kuma ma'aikacin gidan", Kwankwaso ya shaida wa BBC.
A zaben game-gari da ya gabata ya mara wa tsohon mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje baya.
Sai dai tun lokacin da Ganduje ya zama gwamna ake ta sa-toka-sa-katsi tsakaninsa da Kwankwaso.
Rigimar ta yi tsananin da Kwankwaso ya nisanci jihar Kano, inda aka yi yunkurin disashe tauraruwarsa ta hanyar kirkirar kungiyar Gandujiyya wadda mabiyanta ke saka shudiyar hula.
A jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya, jihar da ta fi kowace samar da man fetur, yawancin mutane sun yi amannar cewa babban uban gidan siyasa shi ne, Sanata Godswill Akpabio, wanda yake rike da kujerar majalisar dattawa a halin yanzu.
A matsayinsa na tsohon gwamna, yana da tasiri sosai a jihar.
Wannan ya sa lokacin da ya koma jam'iyyar APC ake ganin jam'iyyar za ta iya samun nasararta ta farko a jihar tun bayan da kasar ta koma tafarkin dimokradiyya a shekarar 1999.
Hasashen hakan ya kara tabbata ne lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi jihar Akwa Ibom a matsayin jihar da zai fara kaddamar da yakin neman zabensa a watan Disamba.
Kuma akwai alamun cewa wata kila kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Bayan wani gangami, na tambayi wasu magoya bayan jam'iyyar APC wadanda suka ce Sanata Akpabio zai kawo wa sabuwar jam'iyyarsa kuri'u 300,000.
Sai dai sanatan ya musanta cewa yana da babban tasiri a siyasa: "Idan wani ya ce maka ni uban gida ne a siyasa, to wannan ba gaskiya ba ne."
"A lokaci guda ne kawai na taba taka rawar mai kama da ta uban gida wato a shekarar 2015. Na goyi bayan gwamnan [jihar Akwa Ibom] mai ci kuma da na gabatar da shi ga mutane, sai ya samu goyon baya," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Sai dai wani dan jam'iyyarsa ya ce nasarar da aka samu a zaben 2015 tana tattare da kura-kurai da tashe-tashen hankula , wanda a cewarsa Mista Akpabio ne ya kitsa su.
Mista Umana Okon Umana, wanda ya nemi zama gwamna a lokacin, ya ce MistaAkpabio yana amfani da hukumomin gwamnati ciki har da jami'an tsaro don dora dan takararsa kan karagar mulki.
Ya bayyana hakan da cewa " wani abu ne da miji da mata suke zama don su rubuta sunan wadanda za su fafata a zaben gwamna da na 'yan majalisar jiha."
Ya ce: "Suna rubuta sunayen ne kafin zabukan fidda gwani. Kuma idan ba ka cikin wadannan 'yan takara za su tabbatar da cewa ba ka halarci wurin da za a yi su ba."
Sai dai wani hukuncin kotun koli a shekarar 2015, ya bayyana zaben a matsayin wanda aka yi cikin 'yanci da adalci.
Yadda siyasar "uban gida" take baci.
Shugaban majalisar wakilan Akwa Ibom, Onofiok Luke, wani tsohon wanda Mista Akpabio yake goya wa baya ne.
Wani mai bin addini sau da kafa, ya dangata nasararsa ga Ubangiji, sai dai wasu da dama na ganin akwai rawar da uban gidansa na siyasa ya taka.
A baya, wani mai taimaka wa Mista Akpabio, ya amsa cewa ya samu taimakon kudi lokacin aurensa da kuma bikin cikarsa shekara 40 a duniya.
Kuma Mista Akpabio ya rika ambato sunansa lokacin tasowarsa a siyasance.
Sai dai sun raba gari kuma shugaban majalisar Akwa Ibom wanda ya ce an taba yi mai tayin ba shi dala miliyan 5.5 don ya sauya jam'iyyarsa.
"Na yi aiki da shi kuma na san yadda yake amfani da hukumomin gwamnati," in ji shi.
A wata wasikar martani daga ofishin yada labaransa ya fitar, Mista Akpabio ya musanta zargin, inda ya ce: "Sun ce sun fahimci cewa wannan lokaci ne na yakin neman zabe kuma ana samun zarge-zarge da yarfe da ake jefa wa abokan adawa."
Son-kai
Yayin da wadanda ake mara wa baya suka dafe madafan iko sukan raba gari nan take da iyayen gidan nasu.
Dokta Ashiru ya ce a kasashe masu tasowa kamar Najeriya an fi samun kudaden shiga a matakin jihohi shi yasa kowa ke rige-rigen samun nasara.
Sai dai kuma Emmanuel Onwubiko na Human Rights Writers Association Of Nigeria ya ce ai son-kai ya fi yawa a harkar siyasa a Najeriya.
"Wadansu iyayen-gidan ba suna yi ba ne don kudi, suna yi domin a girmama su yayin da suka shigo jihohinsu tare da yi masu bambadanci", in ji shi.
Shi kuwa Dr. Ashiru cewa ya yi "babbar matsalar ita ce cewa son-kai ya fi yawa a siyasar uban-gida.
"Dimokradiyya ta al'umma ce, amma wasu tsurari ne ke daukar matakan yadda siyasar ke tafiya musamman abin da ya shafi nadin mukaman siyasa.
"Saboda haka irin wannan tsarin ba zai taimaka wa dimokradiyya ba."
Duk dan siyasar da na yi magana da shi game da siyasar uban-gida sai ya kawar da kai tunda dai ta kunshi tilasatawa da kuma abubuwan da suka ci karo da dimokradiyya.
A yayin da wadanda ake mara wa baya ke kara samun gindin zama babu wani tabbaci kan tsawon lokacin da ludayin iyayen-gida zai ci gaba da zama a kan dawo.
Nan gaba kadan ne Kwankwaso da Akpabio za su tabbatar cewa ko tasirinsu yana da rauni.