Mutane da dama sun mutu a hatsarin jiragen ruwa a Djibouti

Akalla mutum 28 ne suka rasa rayukansu bayan wasu jiragen ruwa biyu sun nutse a gabar tekun Djibouti.
Hadarin ya faru ne minti 30 bayan da jiragen suka sha lodin da ya wuce kima a daidai lokacin da suke barin gabar tekun dake Godoria a ranar Talata.
Wani da ya tsira da ransa ya shaida cewa kusan su 130 ne a jirgin nasu amma bai san ko mutum nawa ba ne a dayan jirgin.
Ana dai gudanar da aikin ceto ga wadanda lamarin ya rutsa da su.
Djibouti dai a 'yan kwanakin nan ta zama mahada ga 'yan cirani musamman masu ketarawa zuwa kasashen larabawa domin aikatau.







