Amurka za ta kalubalanci China da Rasha

Xi Jinping da Donand Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Xi Jinping da Donand Trump

Amurka ta bayyana aniyarta ta kalubalantar karuwar karfin fada aji da kasashen China da Rasha ke da shi a duniya, musamman ma a nahiyar Afirka.

Mai ba shugaban Amurka shawara kan batutuwan tsaro, John Bolton, ya zargi kasashen biyu da kokarin dilmiyar da kasashen Afirka cikin nauyin bashi da kuma dakile muradun Amurka.

A karkashin wannan sabon tsarin Amurka na da zummar fadada karfin fada ajin da take da shi a yankunan duniya da kasashen biyu ke dab da kwacewa daga hannunta.

Ta kuma ce dukkan ayyukan tallafi da take yi da ayyukan da dakarunta ke yi na tsaro da kuma batun tsaron cikin gida na fuskantar hatsari saboda bunkasar karfin ikon da kasashen ke da shi a nahiyar ta Afirka.

Vladmir Putin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladmir Putin

A misali a Djibouti, China ta kafa wani sansanin sojoji kusa da na Amurka, kuma tana da shirin bude wata babbar tashar jirgin ruwa a kasar.

Mista John Bolton ya kuma ce tallafin da Amurka ke bayar wa ga kasashen Afirka zai kasance wani makami na rage karfin fada ajin da kishiyoyin nata ke da shi.

Ana ganin abu na farko da wannan matakin zai fara shafa shi ne shirin nan na tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Amurkar ta dade tana sukar tasirinsa.