Za mu kera makamai masu linzami idan Amurka ta kera- Putin

Russian President Vladimir Putin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Amurka na so ta fake da tuhumar ne don ta janye daga yarjejeniyar

Shugaba Vladimir Putin ya yi gargadin cewa Rasha za ta kera makamai masu linzami da aka haramta amfani da su a wata yarjejeniya da aka sa hannu tun lokacin yakin cacar baka, idan Amurka ba ta mutunta yarjejejniyar daina kera makaman ba.

Kalaman na sa sun zo ne bayan zarginsa da kungiyar tsaro ta NATO ta yi ranar Talata na cewar Rasha ta riga ta karya dokar yarjejeniyar.

Amurka da Rasha sun sa hannu a yarjejeniyar a shekarar 1987, kuma yarjejeniyar ta haramta wa kasashen biyu amfani da makamai masu linzami.

Sai dai Mr Putin ya ce Amurka na so ta janye daga yarjejeniyar ne shi ya sa ta fake da yi wa kasarsa sharri.

A wani jawabi da ya yi wanda aka nuna gidan talabijin, Shugaban Rashar ya ce kasashe da dama sun kera makaman da yarjejeniyar ta haramta.

"Yanzu kamar Amurka ta yi imanin cewa lamarin ya sauya ne sosai da har suke ganin dole su kera wannan makami", a cewarsa.

"Me za mu ce? Abu ne mai sauki- idan suka yi mu ma za mu yi."

A baya dai shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa za ta janye daga yarjejeniyar saboda ayyukan Rasha.

Masana sun ce Rasha na ganin cewa kera makaman zai fi arha kan sauran kayan yaki da aka saba amfani da su.

Me Nato ta ce?

Ranar Talata ne kawancen rundunonin kasashen yamma suka tuhumi Rasha da saba wa yarjejeniyar.

Sanarwar ta ce kasashen suna matukar goyon bayan matsayin Amurka na cewa Rasha ta saba wa yarjejeniyar, kuma ta yi kira ga Rashar da ta gaggauta gyara ayyukanta.

A Russian missile is fired during military exercises

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rasha ta musanta kera makamai masu linzami
Presentational grey line

Mece ce yarjejeniyar makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango? , wadda Amurka da Rasha suka sanya wa hannu?

Mikhail Gorbachev and Ronald Reagan signing the INF Treaty in 1987

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Mikhail Gorbachev da Shugaban Amurka Ronald Reagan sun sa hannu kan yarjejeniyar INF a 1987
  • Amurka da Rasha sun sanya hannu a kanta a 1987, kuma ta haramta amfani da makamai masu guba da makamai masu linzami masu amfani da gajeru da matsakaitan zango, sai dai makaman da ake saki a teku.
  • Amurka ta nuna damuwarta bisa girke makamai masu linzami samfurin SS-20 da Rasha ta yi, kuma ta maida martani ta hanyar girke makamai masu linzami a Turai inda ya janyo zanga-zanga a fadin nahiyar
  • Zuwa 1991, kusan makamai masu linzami 2,700 ne aka lalata
  • Kasashen biyu sun dudduba makaman juna
  • A shekarar 2007, Shugaba Vladimir Putin ya ayyana Rasha bata ra'ayin yarjejeniyar
  • Matakin ya zo ne bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar Makamai masu linzami a 2002
Presentational grey line