Amurka ta bude ofishin jakadancin ta a Somaliya

Asalin hoton, Reuters
Kasar Amurka ta sake bude offishin jakadancinta a Somaliya bayan ofishin ya shafe kusan shakara 30 a rufe.
Amurkar ta bayyana cewa wannan abun tarihin yana bayyana irin cigaban da kasashen Afirka ta gabas suke samu.
Amurka ta kulle ofishin jakancinta a Somaliya a shekarar 1991 a lokacin da ake tsakiyar yaki tsakanin 'yan tawaye da gwamnati.
Hakan ya yi sanadiyar Amurka ta janye Jakadanta da Ma'aikatanta a kasar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kara fadada yakin da ake yi da kungiyar Al-Shabab a shekarar 2017, inda dakarun Amurka suka kai hare-hare sama da 24, wanda hakan ya hada da amfani da jirgi mara matuki domin kai hare-haren a wannan shekarar.
Tarihi ya nuna cewa, shugabanin kasar Amurka na baya suna kauce wa tsoma bakinsu a rikicin Somaliya tun bayan kashe dakaru na musamman na Amurka guda 18 da aka yi a Mogadishu a shekarar 1993, wanda aka yin Fim mai taken "Black Hawk Dawn" a kan wannan yaki na Somaliya.






