Yunwa ta kashe mutum 26 a Somalia

Asalin hoton, AFP
Shafin intanet na gidan rediyon gwamnatin Somaliya ya wallafa cewa a kalla mutum 26 sun mutu sakamakon yunwa a Jubaland da ke yankin Kudancin kasar.
Shafin ya ambato ministan cikin gida na yankin da shugaban kwamitin da ke kula da al'amuran fari, Abdirahman Mohamed Hussein, na cewa an yi mace-macen ne a cikin sa'oi 36.
Ya bukaci a yi taimako na gaggawa domin a shawo kan matsalar yunwa, a cewar gidan rediyon kasar.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres, wanda ya kai ziyara a cikin wannan watan, ya ce kusan mutum miliyan shida ne ke bukatar agaji.
Kasar na fama da matsanancin fari wanda ya yi sanadiyar mutuwar dabbobi kuma ya sa rijiyoyi da koguna suka kafe, kuma hakan ya sa aka kasa yin noma.
Daruruwan iyalai sun bar Jubaland, yayin da suke neman mafaka a Mogadishu, babban birnin kasar.

Asalin hoton, AFP
Baya ga hukumomin agaji na kasa da kasa, wani jarumin Hollywood, Ben Stiller, na daga cikin wadanda ke kokarin samar da kudi domin taimaka wa wadanda ke fama da yunwa a Somaliya.
Ya hada kai da jaruman kafafen sada zumunta domin a samar da dala miliyan biyu a cikin kasa da mako guda.
Wata kungiyar fafutuka mai suna Love Army Campaign, wadda da farko ta bukaci dala miliyan daya domin aikewa da kayayyakin agajin ta jirgin sama, ta hada da wani sanannen mai amfani da kafafen sada zumunta Jerome Jarre da Casey Neistat da Chakabars har da dan wasan kwallon kafar Amurka, Colin Kaepernick.










