Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kun san jaruman da ba sa amfani da shafukan sada zumunta?
Kusan za a iya cewa a yanzu mutane ba jarumai kadai ba na amfani da shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Instagram da Whatsapp da Snapchat da kuma Twitter.
Mutane da kan yi amfani da wadannan shafuka ne wajen sada zumunta da 'yan uwa da abokan arziki, ko kuma saka hotunansu kai har ma yadda suke gudanar da al'amuransu na yau da kullum domin nunawa masu bibiyarsu halin da suke a kowacce rana.
Ga jarumai kuwa, sukan yi amfani da irin wadannan shafuka ne wajen yada halin da suke ciki, ko sun yi tafiya, ko wajen daukar fim ko abincin da suke ci ko kuma iyalansu.
A kasar Indiya ma jarumai kan yi amfani da irin wadannan kafafe, to amma kuma akwai wadanda su sam ba sa amfani da wadannan shafuka, duk da tasirin da suke dashi a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ga wasu daga cikinsu
Aishwarya Rai Bachchan
Duk da kasancewar mijinta Abhishek Bachchan da kuma sirikinta Amita Bachchan ma'abota shafukan sada zumunta ne, Aishwarya ta dakatar da amfani da shafukan sada zumunta gaba daya.
Bata bayyana dalilinta ba, amma kuma wasu na ganin ta yi hakan ne saboda ita mai son sirri ce, ba ta fiye so jama'a su san al'amuranta na yau da kullum ba.
Ranbir Kapoor
Iyalansa ma'ana mahaifinsa da mahaifiyarsa har ma da 'yar uwarsa suna son amfani da kafafan sada zumunta musamman Instagram, to amma kuma mahaifinsa Rishi Kapoor shi ya fi amfani da Twitter.
Yana daga cikin matasan jaruman Indiya da ke tashe a yanzu wadanda ba sa amfani da kowacce kafar sada zumunta.
Yana kuma ganin kasancewarsa haka yafi masa dadi.
Rani Mukherjee
Rani ta kauracewa amfani da shafukan sada zumunta ne, saboda mijinta ba ya sha'awa, ma'ana dai baya so a rinka a ganin hotuna ko kuma a san halin da suke ciki musammamma 'yarsu Adira.
Wannan dalili ya sa Rani duk da kasancewarta fitacciyar jaruma, wadda kuma ta ke da dumbin magoya baya bata amfani da shafukan sada zumunta.
Saif Ali Khan
Duk da yake matarsa Kareena Kapoor da 'yarsa Saira Ali Khan ma'abota shafukan sada zumunta ne musamman Instagram, Saif shi sam bashi da ra'ayi.
To amma duk da haka ana ganinsa akai-akai idan sun yi wata tafiya tare da matarsa ko kuma sun je wajen wani taro tare matarsa Kareena ta dora a shafukanta na sada zumunta.
Wannan ya sa duk da ya kauracewa shafukan, masu bibiyar al'amuransa suna ganinsa akai-akai da ma sanin halin da ya ke ciki.
Aditya Chopra
Shi ma kamar matarsa Rani Mukherjee, ya tsame kansa daga amfani da shafukan sada zumunta.
Aditya ko da ya ke ba jarumi bane, amma fitaccen mai bayar da umarni a fina-finan Indiya domin ya shirya tare da bayar da umarnin fitattun fina-finai kamar Dilwale Dulhania Le Jayenge da Mohabbatein da Dhoom da Veer-Zaara da kuma Ek Tha Tiger da dai sauransu.
Aditya na son sirri musamman a kan abin da ya shafi iyalansa, don haka ya tsame kansa daga amfani da shafukan sada zumunta.