Dalilan rabuwar wasu jarumai da matansu

Akwai wasu daga cikin jaruman fina-finan Indiya da suka yi fice da suka rabu da matansu na farko bisa wasu dalilai.

Sanjay Dutt da matarsa ta farko Rhea Pillai

Rhea ta kasance matar Sanjay Dutt ta biyu, ta aure shi ne bayan rasuwar matarsa ta farko Richa Sharma.

Sanjay Dutt ya rabu da Rhea ne saboda cin amanarsa da ta yi, inda ta ke soyayya da wani mutum na daban.

Yanzu yana tare da matarsa ta uku Maanayata, wadda suke da 'ya'ya biyu tare, suna kuma zaman lafiya.

Saif Ali Khan da Amrita Singh

Saif Ali khan ya auri jaruma Amrita Singh ne tun yana da shekara 21, wanda ita kuma a lokacin da suka yi auren tana da shekara 33.

Akwai bambamcin shekara 12 a tsakaninsu, amma kuma duk da haka ya aure ta saboda biyayyar iyaye.

Bayan sun yi aure sun haifi 'ya'ya biyu mace da namiji, wato Sara da Ibrahim.

Daga bisani sun rabu, saboda dalilai na cewa Saif na neman wata baturiya wato Rozza Catalano.

Yanzu dai Saif ya sake aure inda ya auri Kareena Kapoor, har ma sun haifi da daya Taimur.

Aamir Khan da Reena Dutta

Aamir Khan ya auri Reena Dutt tun a 1986, inda har suka haifi 'ya'ya biyu, mace da namiji.

Amma a 2001, sun rabu bayan jita-jitar da aka rinka yadawa cewa Aamir Khan din na soyayya da jarumar da suka fito tare a cikin fim din Dil Chahta Hai Preity Zinta.

Bayan wannan dalili kuma, akwai dalilin cewa suna da bambamce-bambamce a halayyarsu ko kuma a zamantakewar su, inda shi Aamir ke da zafin zuciya, ma'ana saurin hasala.

Yanzu dai Aamir ya sake aure inda ya auri Kiran Rao, har ma sun fi haifi da daya.

Karishma Kapoor da Sunjay Kapur

Karishma Kapoor ta auri mijinta na fari a 2003.

Sunjay Kapur hamshakin dan kasuwa ne, sun kuma zauna tare na tsawon shekara 13.

Sun haifi 'ya'ya biyu, mace da namiji.

A yayin zamantakewarsu, Sanjay saboda dan kasuwa ne yana yawan tafiye-tafiye, Karishma kan jima bata sanya shi a idanunta ba, hakan ya fara sanya zargi a ranta cewa yana neman mata.

A haka dai, suka fara samun matsala, inda har Sunjay ya ce ta aure shi don kudinsa, kalaman da ba su yiwa mahaifin Karishma Randhi Kapoor dadi ba.

A haka dai rigimar yau daban, ta gobe daban, har suka rabu a 2016.

Bata sake aure ba har yanzu, kuma 'ya'yan na hannunta sai dai suje suga mahaifinsu jefi-jefi.

Hrithik Roshan da Sussanne Khan

Hrithik Roshan sun yi auren soyayya da matarsa, kuma sun haifi 'ya'ya biyu duk maza.

To sai dai kuma mutane sun kadu bayan da suka samu labarin cewa matar ta kai shigar da shi kara inda ta ke bukatar da ya saketa.

Dalilinta kuwa shi ne soyayyar da ya ke da jaruma Kangana Ranaut.

Har yanzu dai bai sake aure ba.

Arbaaz Khan da Malaika Arora

Arbaaz da matarsa Malaika, ma'aurata ne da suke burge kowa, don haka ko da mutane suka ji labarin rabuwarsu sun kadu matuka.

Ba wani abu bane ya raba su face soyayyar da Malaika ta ke yi da jarumi Arjun Kapoor, bayan gashi ta na da aure, hakan ya sa Arbaaz ya ga ta ci amanarsa ya kuma sawwake mata.

Suna da 'ya'ya biyu duk maza.

Karanta wasu karin labaran.