Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tura sojoji da jirgin yaki zuwa Sokoto
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta tura sojoji da jirgin yaki da makamai zuwa Sokoto domin yaki da 'yan fashi da masu satar mutane.
Sanarwa da kakakin rundunar sojin sama Ibikunle Daramola ya tura wa manema labarai, ta ce an tura dakarun ne tare da jirgin yaki domin taimakawa rundunar Operation Diran Mikiya da ke yaki da 'yan bindiga tsakanin kan iyakar Sokoto da Zamfara da Katsina
Tuni sojojin suka isa Sokoto a ranar Lahadi domin soma yaki da 'yan fashi da suka addabi yankin na arewa maso yammacin Najeriya.
Babban kwamandan sojin sama a Sokoto Air Vice Marshal Oladayo Amao da ya tarbi sojojin, ya bukaci su nuna kwarewa ga aikin da aka turo su na tabbatar da tsaron al'umma da kuma yakar 'yan fashi.
Sanarwar ta kuma ce za a inganta filin jirgin Sultan Abubakar III a Sokoto da dukkanin abubuwan da suka wajaba domin kaddamar da hari ta sama daga tashar jirgin saman.