Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama 'yan bindigar da suka sace 'yan mata tagwaye a Zamfara
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama gungun 'yan fashi masu satar mutane a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sandan Jimoh Moshood, ta ce ta kama mutum 12 da suka yi garkuwa da wasu tagwaye 'yan mata a watan Oktoba.
An cafke su ne a mabuyarsu tsakanin Zamfara da Katsina, in ji sanarwar.
'Yan fashin sun kuma amsa cewa sun dade suna fashi da makami da satar shanu da kuma satar mutane domin kudin fansa.
Daga cikin barayin 12 da aka kama har da mai shekara 60 da kuma wasu guda biyu masu shekara 56.
Sauran barayin daga shekara 28 zuwa 40, kuma dukkaninsu 'yan asalin jihar Zamfara ne.
Barayin sun tabbatar wa 'yan sanda cewa sun karbi naira miliyan 15 kafin su saki tagwayen 'yan matan, inda suka raba, kowa ya karbi naira 500,000.
An sace 'yan matan ne a ranar 21 ga watan Oktoban 2018 a garin Dauran na jihar Zurmi, lokacin da suka tafi raba goron gayyatar bikin aurensu.
Sanarwar ta ce bayan sace 'yan matan ne, 'yan sanda suka shiga gudanar da binciken sirri domin kama 'yan bindigar.
'Yan sandan sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin cafke jagoran 'yan bindigar da ake kira Dankarami da wani Sirajo dogo da suka jagoranci sace 'yan matan.
'Yan sandan sun samu manyan makamai hannun barayin da suka hada da bindiga kirar AK47 guda shida da albarusaai na AK47 34 da takobi hudu.
Za a gabatar da su kotu bayan 'yan sandan sun kammala gudanar da bincike.