Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin EFCC ta kama alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen?
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta musanta rahotannin da ke cewa ta kama alkalin alkalan kasar Walter Onnoghen.
Ana tuhumar mai shari'a Onnoghen da zargin yin karya wajen bayyana kaddarorin da ya mallaka.
A ranar Litinin ne kotun da'ar ma'aikata ta soma sauraren tuhumar da ake yi masa, ko da yake bai gurfana a gabanta ba saboda, a cewar lauyoyinsa, ba a mika masa sammaci ta hanyar da ta dace ba.
Sai dai wasu rahotanni sun ambato EFCC na cewa ta kai samame gidan alkalin alkalan na Najeriya inda ta yi awon gaba da shi.
Amma a sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta musanta labarin, tana mai cewa labarin karya ne.
"An jawo hankalin EFCC kan labarin karya da ake watsa wa a shafukan sada zumunta cewa EFCC ta kama alkalin alkalan Najeriya, Mai shari'a Walter Onnoghen.
Wannan ba komai ba ne face zugitamalle daga wurin masu yada labaran karya. Muna so a sani cewa EFCC ba ta je gidan alkalin alkalai domin ta kama shi ba kuma ba ta aike masa da gayyata a game d hakan ba."
Abin da ya sa aka dabe shari'ar Walter Onnoghen
Kotun da'ar ma'aikata ta dage zamanta na sauraron shari'ar da ake yi wa Alkalin Alkalan na Najeriya Mai shari'a Walter Onnoghen, bayan ya ki bayyana a gaban kotun a ranar Litinin.
Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Sai dai babban alkalin ya tura wasu manyan lauyoyi 47 wadanda suka wakilce shi.
Lauyoyin babban alkalin sun ce bai bayyana ba ne saboda ba a mika wa mutumin da suke karewa takardar sammaci a hannunsa ba.
Sun kara da cewa kotun ba ta da hurumin sauraren shari'ar.
Daga nan ne kotun ta dage zamanta har zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun.