An ci gaba da lugudan wuta a Yemen duk da yarjejeniya

Asalin hoton, AFP
Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da a ka cimma kwanan nan, rahotanni sun ce an ci gaba da lugudan wuta ta sama, tare da bata-kashi a garin Hodeidah mai tashar jiragen ruwa na Yemen.
Ana bata-kashin ne tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Houthi.
Majiyoyin gwamnati sun ce an kashe akalla mayaka ashirin da tara a daren Asabar, akasarinsu 'yan tawayen Houthi.
Jami'ar bayar da agajin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Yemen, Lisa Grande ta shaidawa BBC cewa har yanzu ta na da kyakkyawar fata, yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma a Sweden za ta yi tasiri.
Mataimakin ministan yada labarai na 'yan tawayen Houthi ya ce yarjejeniyar za ta fara aiki daga ranar Laraba.
Duk kan bangarorin dake fadan za su janye mayakansu a cikin 'yan kwanaki da fara aiki da yarjejeniyar.







