'Yan sandan Najeriya baki har kunne saboda karin albashi

Farin ciki ya rufe 'yan sandar Najeriya sakamakon labarin da suka samu da ke nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da yi musu karin albashi mai gwabi.

Tuni dai wasu daga cikinsu suka fara lissafin irin abubuwan da suke sa ran yi da zarar sabon albashin ya shiga aljufansu.

Wakilin BBC ta ziyarci hedikwatar `yan sandan jihar Kano, ya ce daga ganin irin yadda suke fareti, to akwai wata annushuwa a tare da su.

Wasu daga cikin 'yan sandan da BBC ta tattauna da su sun ce, duk da albashin bai fara isowa gare su ba, labarin karin ma babban abin farin ciki ne, saboda maganar karin albashin ta fito ne daga bakin da ba ya karya wato bakin shugaban kasa.

Wata 'yar sanda da wakilin BBC ya tattauna da ita ta ce' A gaskiya muna farin ciki da wannan al'amarin, saboda a yanzu ne muka san muna aiki, sannan zamu ji dadin aikinmu sosai, kuma ko shakka babu yanzu zamu kara kwazo a aikinmu'.

Shi kuwa wani dan sandan da aka zanta da shi cewa ya yi "Yanzu zanje na bare gidana na saka tailes kamar yadda kowa ke sa wa a gidansa, sannan kuma na saka AC, na ji dadin rayuwata, kuma ada kullum da safe sai dai muci kosai, amma yanzu sai taliya da doya da kwai".

To sai dai kuma a yayin da 'yan sanda magidanta ke murna da wannan karin albashi, tuni hantar matan wasu daga cikinsu ta fara kadawa saboda gudun kada a auro musu abokiyar zama.

A Najeriya dai 'yan sanda na daga cikin hukumomin gwamnati da ake zargi da karbar cin hanci da rashawa, lamarin da masana ke dangantawa da karancin walwala a rayuwarsu.