Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barawo ya bi 'yan sanda har gida ya sace motarsu
Barawo ya je wurin ajiye motoci na ofishin 'yan sandan yankin Suffolk da ke Birtaniya ya sace daya daga cikin motocinsu - kuma basu sani ba sai da wani mutum ya ankarar da su.
An sace motar daukar kayan ce daga ofishin 'yan sanda na Lowestoft ranar Asabar.
Wani mutum ya kira 'yan sandan ta wayar tarho ya shaida musu cewa ya ga wani mutum a cikin motar daukar kayan yana tukin dan koyo da misalin karfe 9:25 na dare a agogon GMT.
Tuni dai 'yan sandan na Suffolk suka karbo motar sannan suka kama mutumin mai shekara 27 da ke zaune a yankin Bungay.
Tukin dan koyo
Wani mutum ya ga barawon a kan hanyar Vauxhall Vivaro zuwa Whapload Road da ke Lowestoft.
Bayan kimanin minti goma wani mutum kuma ya ba da rahoton ganin barawon yana tukin dan koyo a yankin Kessingland zuwa Halesworth.
An gano motar daukar kayan ne kimanin mil 17 daga Bungay da misalin 01:00 ranar Lahadi bayan wani mutum ya kira 'yan sanda.
'Yan sanda sun ce an kama barawon ne da safiyar Lahadi inda ake tuhumarsa da satar mota da sauran laifuka.