Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya aminiyar gaske ce - Trump
A yayin da yake yin tsokaci game da rahoton CIA kan Yarima Bin Salman, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Saudiyya aminiyar gaskiya ce.
Trump ya bayyana rahoton hukumar CIA da ta ce bincikenta ya tabbatar da Yariman Saudiya mai jiran gado ne ya bayar da umurnin kisan Jamal Khashoggi a matsayin wanda bai kammalu ba tare da jaddada girman dangantar da ke tsakanin Saudiyyar da Amurka.
Shugaban ya ce zuwa ranar talata ne ya ke fatan samun cikakken rahoto kan tabbatar da wanda ya bayar umurnin kisan dan jaridar na Saudiya Jamal Khashoggi.
Da yake zantawa da manema labarai a ziyarar da ya kai domin gane wa idonsa girman barnar bala'in wutar daji a jihar California, shugaba Trump ya ce yana tattaunawa da hukumar CIA game da rahoton.
Ya ce ba su tantance komi ba tukuna, an yi gaggawa domin rahoto ne da bai kammalu ba. "Zuwa ranar Talata za mu samu ciakken rahoton," in ji shi.
A ranar Asabar ne dai kafofin yada labaran Amurka suka ruwaito cewa hukumar leken asirin Amurka ta ce bincikenta ya tabbatar da Yariman mai jiran gado Saudiyya Muhammad bin Salman ne ya bayar da umurnin kisan Mista Khashoggi.
Sai dai kuma da yake bayani game da rahoton, shugaba Trump ya jaddada muhimmacin dangantar da ke tsakanin kasarsa ta Amurka da Saudiyya, yana mai cewa Amurka na da kyakkyawar alaka da Saudiyya.
"Sun bamu ayyuka da kasuwanci da yawa da kuma bunkasa tattalin arzikinmu, sun kasance aminan gaskiya ta fuskar samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arzikinmu, kuma a matsayi na shugaban kasa dole sai na tattauna da CIA"
Gwamnatin Saudiyya dai ta musanta zargin, kuma tuni Amurka ta ce akwai alamar tambayoyi da dama a kan batun kashe dan jaridar na Saudiyya Jamal Kashoggi a watan jiya.
Amurka ta ce za ta tabbatar da ganin wadanda ke da hannu a kisan sun fuskanci hukunci duk da kara jaddada amincinta da Saudiyya.
Shugaba Trump na dada fuskantar matsin lamba game da al'amarin kisan na khashoggi.
Wasu manyan 'yan siyasa a Amurka sun bukaci a gaggauta daukar mataki tun kafin Yariman Saudiyya da ake zargi ya gaggauta kashe mutanen da suka aiwatar da umarnin da ya ba su.