Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurkawa na zaben tsakiyar zango
A wannan talatar Amurkawa ke shirin soma jefa kuri'a a zaben tsakiyar zango, don zaben wadanda za su wakilce su a majalisun kasar biyu.
Jam'iyyar Democrats ta fi raja'a wajen kwace ikon majalisar wakilan kasar, yayin da Republican ta fi matsa kaimi a bangaren majalisar dattawa.
Shugaba Trump ya shaida wa magoya bayansa a Indiana cewa jam'iyyarsa ta Republican na cika burin Amurkawa.
A ziyarar da ya kai jihohin kasar uku, shugaban ya jaddada nasarorinsa a bangaren samar da aiki da bunkasar tattalin arziki da kuma matsayarsa a kan bakin-haure.
A 'yan makonnin nan mista Trump ya zafafa kalamansa a kan masu adawa da shi da kuma batutuwa masu raba kawunan al'ummar kasar kamar batun shige da fice.
Hakazalika har gargadi ya yi wa masu kada kuri'a, a kan shirin jam'iyyar Democrats da ya ce zai iya janyo masu aikata laifi daga yankin tsakiyar nahiyar Amurka su mamaye kasar.
Mista Trump ya kuma yi barazana ga masu zabe cewa, idan har jam'iyyar Democrats ta samu galaba to lallai ba shakka za a samu tudadowar bakin-haure cikin kasar wanda hakan kuma zai janyo samun aikata manyan laifuka a Amurka.
A bisa al'ada dai lokutan irin wannan zabe ba kasafai mutane ke fita domin kada kuri'unsu ba a kasar, amma a wannan karon masu sharhi sun ce akwai yiwuwar a samu fitowar masu kada kuri'a fiye da shekarun baya.