Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a yi zaben tsakiyar zango a Amurka kwanan nan
Shekara biyu bayan da aka yi zaben da ya shigar da Shugaba Donald Trump fadar White House, Amurkawa za su sake kada kuri'a ran 6 ga watan Nuwamba.
Sai dai wannan karon za su zabi 'yan majalisun dokoki ne. Yadda za su kada kuri'un na da muhimmanci ga ragowar shekaru biyun da suka rage wa Shugaba Trump a mulki.