Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya ta nesanta yarimanta da mutuwar Khashoggi
Kasar Saudi Arabia ta ce yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga dan Jamal Kashoggi, dan jaridar nan dan kasar da aka kashe a ofishin jakadancin Saudiyyan da ke Santanbul na kasar Turkiyya.
Ministan harkokin wajen Saudiyyan dai ya hakikance cewa, yarima mai jiran gadon bashi da wata masaniya a game da abinda ya yi sanadiiyar mutuwar dan jaridar.
Saudiyya na fuskantar matsin lambar diflomasiya a kan ta fadi gaskiyar abin da ya faru da Mista Khashoggi kusan makonni uku, bayan musanta rahotannin farko da aka ce ya mutu.
Wakilin BBC ya ce Saudiyya na kokari nuna cewa ta damu matuka da abin da ya faru kuma ta na kokarin dauke hankulan mutane daga zargin da ake yi na hannun yariman a kisan.
Kasashe irinsu Birtaniya da Jamus da Faransa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ta bayyana kaduwarsu a kan kisan dan jaridar da kuma bukatar karin bayani a kan kisan.
Sai dai yayin da wasu kasashe ke barazanar yanke wasu hulda da kasar ta Saudiyya, su kuwa kasashen labarawa kamar Kuwait da Masar da Bahrain da kuma Hadaddiyar daular Larabawa, jinjina wa Sarki Salman suka yi a kan yadda ya tunkari batun.
Turkiyya dai ta yi wa kisan Mista Khashoggi wata fahimtar ta daban, kuma ita ce ta tun farko ta fara cewa an kasashe a ofsishin jakdancin Saudiya da ke kasarta har ma ta ce tana shaida akai.