Yariman Saudiyya: Shin ruwa ya kare wa dan kada ne?

    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan sha'anin tsaro

Kasa da wata 18 ke nan da jirgin saman Shugaban Amurka ya sauka a Riyadh, inda ya samu gagarumar tarba.

Lokacin da Shugaba Trump ya zabi Saudiyya ta zama kasar da zai fara kai ziyararsa ta shugaban kasa a watan Mayu na shekarar da ta wuce, 'yan kasar Saudiyya da dama sun yi matukar murna da farin ciki.

Ba su damu sosai da mutumin da Trump ya gada ba, wato Barack Obama.

Suna ganin ko alama bai damu sosai da yankin Gabas ta Tsakiya ba, kuma abin da ya bari na tarihi na yarjejeniyar nukiliya da Iran abu ne maras kyau a wurinsu.

To amma suna ganin Donald Trump mutum ne da za su yi harka da shi. Ya cire musu takunkumin da gwamnatin Obama ta sa musu na hana sayar musu makamai saboda yakin Yemen.

Ya bar matsa musu a kan 'yancin dan adam, sannan kuma bisa ga dukkan alamu yana farin cikin yadda surukinsa Jared Kushner ke kulla kyakkyawar alakar aiki da Yarima Mai jiran gado mai karfin fadi a ji na Saudiyya Mohammed Bin Salman.

Bayan nan ne kuma sai shi ma Yarima Salman wanda ake masa lakabi ba MBS, ya mayar da ziyarar inda ya je fadar gwamnatin Amurka, White House da Ma'aikatar tsaro, Pentagon da kuma cibiyar yin fina-finan Amurka, Hollywood.

Haka kuma an yi maraba da shi a Landan, duk da zanga-zangar nuna adawa da yaki da aka shirya a kan yadda yake aiwatar da hare-hare kan rikicin Yemen, wanda ke haddasa asarar rayuka da jefa mutane cikin bala'i.

A gida Saudiyya jami'an diflomasiyya na kasashen Yamma sun yaba da sauye-sauyen da Yariman ya bullo da su na zamanantar da kasar da cewa 'yanci ne na walwala da kasar ta dade tana bukata.

Daga cikin sabbin matakan da ya bullo da su, ya dage dokar hana mata tukin mota, ya dawo da abubuwa na walwala da nishadi, kamar wasu wasanni da sinima, sannan kuma ya rage ikon 'yan sandan Hisbah.

Haka kuma a wannan lokacin ne ya bayyana wani babban buri na kawar da kasar daga dogaron da take ga mai ta hanyar gina wani katafaren birni na zamani a hamada wanda za a kashe dala biliyan 500 wurin gina shi.

A karkashin tsarinsa Saudiyya na ganin sauye-sauye wanda bara a daidai wannan lokacin, manyan 'yan kasuwa da jami'an gwamnatoci da shugabanni daga kasashen duniya suka rika tururuwa domin halartar taron da ya shirya na zuba jari domin aiwatar da tsare-tsaren bunkasa kasar da yake hange, a Riyadh.

Abubuwa da dama sun sauya a kasar

Sai dai tun kafin tafiya ta yi nisa sai aka fara ganin alamun da suka nuna cewa Yarima Salman din dai kila ba shi ba ne mai sauyin da kasashen Yamma ke fatan gani.

Hakan kuwa ya kasance ne bayan da kwatsam ya shiga sanya wa ana kamawa tare da tsare gomman 'yan gidan sarauta da manyan 'yan kasuwar kasar a shekarar da ta wuce a wani otal na alfarma, yana zarginsu da cin hanci da rashawa.

Har ma sai da ya tsare Firai Ministan Lebanon Saad Hariri na dan wani takaitaccen lokaci, inda ake zargin ya tilasta masa da ya yi murabus.

Ya kuma rika bayar da umarnin a kama duk wanda ya soki lamirin tsarinsa na sauye-sauyen da yake yi ko da kuwa, dan wani rubutu ne mutum ya yi a Twitter.

To amma babban zargin da ake yi na bacewar babban mai sukar lamirinsa Jamal Khashoggi, a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Turkiyya ranar biyu ga watan Oktoba.

Wannan ya sa hatta abokinsa mafi kusanci Donald Trump ya yi barzanar daukar mataki mai tsanani a kan gwamnatin Saudiyyar idan har ta tabbata tana da hannu a zargin kisan dan jaridar.

Nan da nan a ranar Lahadi, Saudiyyar ta bijiro da cewa ita ma za ta iya ramawa ta ruwan sanyi, tana mai tuna wa duniya irin muhimmanci da karfin da take da shi a kasuwar mai ta duniya.

'Yan kasar ta Saudiyya da dama bisa kwarin guiwa da goyon bayan da kafofin watsa labarai na gwamnatin kasar ke bayarwa suna nuna cewa lalle su kam suna tare da gwamnatinsu.

Akwai ma wata jita-jita da ke bazuwa a kasar cewa abin da ya faru a Santanbul a kan wannan dan jarida, shiri ne kawai da Turkiyya da Qatar suka yi domin kawai su bata wa gwamnatin Saudiyyar wadda ba ta da alhakin kowa suna.

To amma kuma akwai wadanda a asirce suke ganin cewa anya kuwa wannan Yarima mai shekara 33, mutumin da a da ake daukarsa a matsayin mai hangen nesan da zai ceto Saudiyya bai wuce gona da iri ba?

Da farko dai ya jefa kasarsa cikin yakin da ke lakume dimbin dukiya da rayuka wanda kuma da wuya ta yi nasara a kansa a Yemen.

Ya shiga kazamin rikici da makwabciyarsa Qatar, ya raba gari da Canada a kan batun 'yancin dan adam, kana kuma ya kulle gomman jama'a saboda zanga-zangar lumana tare da mayar da wasu 'yan sarautar kasar da 'yan kasuwa da dama saniyar ware.

'Yan kasar ta Saudiyya da dama masu ra'ayin rikau dai za su fi so a ce kasar ba ta kai ga shiga wannan yanayi ba da ke neman tayar musu da zaune tsaye.