Saudiyya ta gaskata mutuwar Khashoggi

Jamal Kashoggi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tun a ranar 2 ga watan nan na Oktoba ne ba a sake jin duriyar Jamal Kashoggi ba

Bayan mako biyu da aka kwashe Saudiyya na musanta zargin da ake mata, a karshe ta fito ta amince cewa dan jaridar nan Jamal Khashoggi kashe shi aka yi a cikin ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul na Turkiyya.

Tashar Talabijin ta Saudiya ta ce Khashoggi ya mutu ne bayan barkewar fada a ofishin jakadancin kasar da shi da wasu, sai dai hukumomin ba su bayyana abin da aka yi da gawarsa ba.

Saudiyya ta fuskanci matsin lambar diflomasiya kan ta yi bayyanin yadda aka yi danjarida Khashoggi ya yi batan-dabo, bayan jami'an Turkiyya sun tabbatar an kashe shi a cikin ofishin jakadancin Saudiyyar, sannan aka yi gunduwa-gunduwa da shi.

Shugaba Trump na Amurka ya bayyana matakin Saudiyyar na bayyana abin da ya faru da Jamal Kashoggi a matsayin matakin farko mai kyau, kana ya nuna gamsuwarsa da bayananta inda ya ce akwai sahihanci a ciki.

Tashar talabijin din kasar ta ce tuni aka kori mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar ta Saudiyya da kuma wani babban mai bayar da shawara ga yarima mai jiran gado a kan wannan batu.

Wannan ne dai karon farko da masarautar Saudi Arabia ta amince da cewa Jamal Kashoggi ya mutu.

Rahotanni sun ce Sarki Salman ya bayar da umarnin a kafa wani kwamiti na ministoci karkashin jagorancin yarima mai jiran gado domin yin garambawul a ayyukan hukumar leken asirin kasar.

Tun a ranar 2 ga watannan na Oktoba ba a sake jin duriyar Jamal Kashoggi ba, bayan ya shiga ofshin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya domin karbar wasu takardu da za su ba shi damar aurar wata budurwa.

Rahotannin daga Saudiyyar a kan mutuwar Jamal sun bayyana ne jim kadan bayan Sarki Salman ya yi waya da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a kan batun.

Wata sanarwa daga mai shigar da kara na kasar Saudiyya ta ce fada ya barke ne tsakanin Kashoggi da kuma wasu mutane da ya hadu da su a cikin ofishin jakadancin lamarin da ya yi sanadiyyar ajalinsa a wajen.

Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma tuni 'yan sanda a Turkiyya suka fadada bincike domin gano gawar Kashoggi.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya damu matuka da wannan abu da Saudiyya ta fada, inda kuma ya jaddada bukatar hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan dan jaridar.