'Turkiyya na da shaida a kan kisan Khashoggi'

Kwanaki 10 kenan rabon da a ji duriyar Jamal Khashoggi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kwanaki 10 kenan rabon da a ji duriyar Jamal Khashoggi

Kafofin yada labaran Amurka sun ce gwamnatin Turkiyya na da hoton bidiyo da muryar da aka nada wadanda suka tabbatar da cewa dan jaridar Saudiyar nan da ya yi batan dabo Jamal Khashoggi, kashe shi aka yi a cikin ofishin jakadancin Saudiyar da ke Santanbul.

An rawaito Jami'an Amurka da Turkiyya na cewa hotunan da aka dauka na tattare da shaidar cewa tawagar jami'an Saudiyya sun tsare Mista Khashoggi a lokacin da ya je ofishin jakadanci don karbar wasu takardu, sannan suka kashe shi.

Saudiya dai ta musanta ta na da hannu a bacewar Mista Khashoggi.

Kamfanonin yada labarai sun janye daga halarta wani taron masu zuwa jari da za a gudanar a birnin Riyadh na Saudiya kasa da makonni biyu masu zuwa, saboda damuwar da ake nunawa a kan batar dan jaridar kasar Jamal Khashoggi.

Yau kwana 10 ba a ji duriyar Mista Khashoggi ba, tun bayan da ya kai ziyara ofishin jakadancin Saudiya da ke birnin Santanbul na Turkiyya.

Kamfanonin yada labaran da suka da jaridar New York Times da The Financial Times da The Economists, sun ce za su kauracewa taron da zai ja hankali da kuma samun halartar manyan jiga-jigai a harkokin kasuwanci a duniya.

A London, Jakadan Saudiya a Burtaniya ya shaida wa BBC cewa ba zai iya cewa komai ba har sai an kammala binciken hadin-gwiwa tsakanin Turkiyya da Saudiyar.

Shugaba Trump dai ya ce ba zai soke cinikin sayar wa Saudiyar makamai ba a kan kudin da suka haura dala miliyan 100, a kan wannan batu.

Mista Trump ya ce, sadaukar da wannan yarjejeniyar ciniki barazana ce ga ayyukan Amurka.

Wani dan majalisar dattawan Amurka Chris Van Hollen, ya ce Amurka kan yi suka idan har aka ci zarafin bil adama a Saudiyya, to amma a wannan karon gwamnatin Trump ba ta cewa uffan ba.

Gwamnatocin baya na da kyakyawar alaka da Saudiyya kuma hakan bai sa sun ajiye akidojinsu ba.