Jamal Khashoggi: Amurka da Burtaniya na iya kauracewa taron Saudiyya

Asalin hoton, Reuters
Amurka da Burtaniya na tunanin kauracewa wani babban taro na kasa-da-kasa a Saudiyya saboda batun bacewar dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi.
MIsta Khashoggi, wanda ya dade yana sukar mahunkuntan Saudiyya, ya bace ne ranar 2 ga watan Oktoba bayan da ya ziyarci karamin ofishin jakadancinta a birnin Santanbul.
Hukumomin Turkiyya na ganin wasu jami'an leken asirin Saudiyya sun kashe shi ne a cikin ofishin jakandancin - batun da Saudiyya ta musanta a matsayin "karairayi".
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi wa Saudiyya "horo" idan aka gano tana da hannu a bacewar mutumin.
Yawancin wadanda suka nuna sha'awar daukar nauyin taron har da kafofin watsa labarai sun janye aniyarsu ta halarta.
Taron da aka shirya gudanarwa a birnin Riyadh, an lakaba masa sunan Davos a Hamada, wani shagube ga halin da MIsta Khashoggi ya ke ciki.
Kafofin diflomasiyya sun shaida wa BBC cewa sakataren Baitulmalin Amurka Steve Mnuchin da sakataren Cinikin Kasa da Kasa na Burtaniya Laim Fox suna tunanin fasa halartar taron.
Yarima Mohamd bin Salman mai jiran gado ne ya shirya taron domin samar da masu zuba jari a shirinsa na zamanantar da daular.
Matar da Mista Khashoggi ke niyyar aura, Hatice Cengiz ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki kwakkwara ida aka tabbatar da mutuwarsa.

Asalin hoton, AFP
Hatice Cengiz ta ce ranar Asabar da ta gabata ce ranar zagayowar haihuwar Jamal Khashoggi.
Ta ce, "Idan mun rasa Jamal, to lallai kalaman sukar masu laifi kasheshi ba za su wadatar ba", a cikin wata wasika da aka wallafa a jaridar New York Times. "Dole ne a hukunta mutanen da suka raba mu da shi, ko da wane dalili ne."
Shugaba Trump ya ce Amurka za ta gallaza wa Saudiyya "mummunan horo" idan daular na da hannu wajen kisan Mista Khashoggi.
Ya ce "hankali zai tashi matuka idan lamarin ya kasance haka."
Mene ne abin da ake zargin ya faru a Santanbul?
Wani masanin harkokin tsaron a Turkiyya ya sanar da BBC cewa jami'an kasar na da hujja ta bidiyo da na sauti da ke tabbatar da an kashe Mista Khashoggi ne a cikin ofishin jakadancin Saudiyyan.
Shi dai Mista Khashoggi yana aiki ne da jaridar Washington Post ta Amurka.
Rahotanni sun ce an yi ta kokawar cin karfinsa a cikin ofishin jakadancin Saudiyyar, bayan da ya tafi can domin karban wasu takardu.
Wata majiya a Turkiyya ta yi zargin wasu jami'an leken asiri 15 ne suka kashe Mista Khashoggin.
Tuni tashoshin talabijin na Turkiyya suka nuna bidiyon lokacin da Mista Khashoggin ke shiga ofishin jakadancin Saudiyyan domin karaba wasu takardu da suka jibancin shirin aurensa da budurwarsa Hatice Cengiz.












