Najeriya ce hedikwatar talauci a fadin duniya – Jonathan

Goodluck Jonathan

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Mista Jonathan shi ne shugaban Najeriya tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce kasar ce hedikwatar talauci da fatara a fadin duniya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a sakonsa na bikin cika shekara 58 da samun 'yancin kan kasar a ranar Litinin, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Bayan ya taya 'yan kasar murnar zagayowar ranar 'yancin kan ne, tsohon shugaban ya yi tsokaci wanda a cewarsa kasar ta zama "hedikwatar fatara da talauci."

Sai dai ya ce hakan ba abu ba ne da zai dore saboda amannar da ya yi cewa 'yan kasar suna da jajircewa.

A karshe ya yi fatan cewa al'amura za su kyautatu da kuma fatan Ubangiji Ya albarci kasar da al'ummarta.

Sai dai kawo yanzu babu wani martani daga fadar shugaban kasar game da ikirarin na tsohon shugaban.

Kuma ba wannan ba ne karon farko da Mista Jonathan ya fara sukar manufofin gwamnatin Shugaba Buhari, wato mutumin da ya gaje shi a shekarar 2015.

Karanta wadansu karin labarai