Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba mu yarda da sakamakon zaben Osun ba —PDP
Babbar jam'iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ta yi watsi da sanarwar da hukumar zaben kasar INEC ta yi cewar ba a kammala zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar a jihar Osun da ke kudu maso yammacin kasar ba.
A wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, kakakin jam'iyyar PDP din, Kola Ologbodiyan, ya ce jam'iyyarsa ta yi imanin cewar dan takararta, Sanata Ademola Adeleke ne ya ci zaben domin shi yake kan gaba bayan ya samu kuri'u 254, 698.
Hukumar INEC dai ta ayyana zaben gwaman Osun din a matsayin wanda ba a kammala ba ne bayan ya bayyana cewar ratar da ke tsakanin PDP da APC bai kai adadin kuri'un da aka soke ba.
Ologbodiyan ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bayyana sharrudan cin zabe, kuma dan takarar jam'iyyar PDP ya cika su, a cewarsa.
Kana kakakin na PDP ya yi ikirarin cewar ayyana cewar ba a kammala zaben ba wata dabara ce wadda jam'iyyar APC ke son amfani da ita wajen cin zabe.
Ya nanata cewar PDP ba za ta amince da sakamakon da INEC ta fitar ba, yana mai kira ga shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauya wannan matakin da hukumar ta dauka.
Sai dai kuma hukumar INEC ta fitar da wata sanarwar da ke cewa za a sake zabe a rumfunar zabe bakwai cikin kananan hukumomi hudu a jihar Osun ranar 27 ga watan Satumba.
Sanarwar da kwamishinan watsa labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar, Sololomon Adedeji Soyebi, ya sanya wa hannu, ta ce kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Ife North da Ife South da Oloru da kuma Osogbo.