Karanta yadda aka yi zaben gwamnan Osun
A nan ne muka kawo karshen wannan labarai da sharhi. Ku karanta yadda aka yi zaben gwamnan jihar Osun.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da sharhi game da yadda ake zaben gwamna a Osun wanda ake ganin zai nun irin yadda zaben 2019 zai kasance a Najeriya.
Abdulwasiu Hassan
A nan ne muka kawo karshen wannan labarai da sharhi. Ku karanta yadda aka yi zaben gwamnan jihar Osun.
Akwai masu zabe kimanin 21 a kan layi a rumfar zabe ta biyar, a mazaba ta hudu a karama hukumar Irepodun a garin Ilobu inda mataimakin kakakin majalisar wakilai, Yusuf Lasun ya kada kuri'a.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar sake cafke wani da ake zargi da sayen kuri'u.
A sanarwar, da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta kama mutumin ne a lokacin da ya sake sayan kuri'u wa jam'iyyarsa ta PDP.
Ta kara da cewar an samu naira 116, 000 a hannunsa.
Sai dai kuma rundunar ta ce har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta yi gargadi ga 'yan Najeriya game da wallafa jabun sakamakon zabe.
Hukumar ta fadi haka ne a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce duk wanda aka samu da wannan laifin zai fuskanci kotu.
Ta kara da cewa ita za ta sanar da sakamakon a hukumance.
An fara kirga kuri'a a mazabun da aka yi zaben gwamna a jihar Osun.
A wannan wurin ne hukumar zaben Najeriya, INEC, za ta bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Osun.
Gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola ya ce shi ba ya tunanin APC za ta samu matsala a zaben gwamnan Osun da ake yi ranar Asabar.
Gwamnan ya yi wannan maganar ne a lokacin da BBC ta tambaye shi game da ko zai tallafa wa duk wani dan jam'iyyun adawa da ya doke APC.
Rauf ya ce shi bai yi tunanin rashin nasara wa jam'iyyarsa ba don, acewarsa, mutanen jihar suna son jam'iyyarsa.
An kammala zabe a rumfar zabe ta hudu a mazabar Boluwaduro da ke Osogbo, kuma ana jiran a kai karfe biyu ne kafin a fara kirga kuri'u.
Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya tura jami'an 'yan sanda 18, 426 jihar domin aiki da sauran jami'an tsaro.
Rumfunar zabe 3,010 ake da su a jihar Osun inda ake zaben gwamna a yau.
Sufeto janar din ya ce akalla za a samu jami'an tsaro hudu a ko wace rumfar zabe a jihar.
Mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya, Yusuf Lasun, ya bayyana ra'ayinsa game da sauya shekar da kakakin majalisar wakilan kasar, Yakubu Dogara, ya yi daga jam'iyyar APC zuwa PDP.
A hirar da ya yi da BBC bayan kada kuri'arsa, Lasun ya ce Dogara abokinsa ne, "amma a siyasa inda mutum ya ga dama zai koma. Babu abin da zai raba mu. Son ransa ne ya sa ya koma tsohuwar jam'iyyarsa. Ni ma ina cikin jam'iyyata."
Daga bisani sai ya bukaci mutanen jihar ya yi zabe lami lafiya ba tare da tashin hankali ba.
Mata sun fito da goyon domin kada kuri'a a zaben gwamnan da ake yi a jihar Osun.
Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya tana fama da wasu matsaloli da suka hada da rashin biyan albashi yadda ya kamata da yawan bashi da kuma matsalar jami'ar kimiyya da fasaha ta Ladoke Akintola da ke Ogbomoso.
Wannan na cikin abubuwa da aka tattauna a muhawarar da BBC ta shirya wa 'yan takarar gwamna a jihar kafin zaben.
'Yan takarar dai sun bayyana shirye-shiryensu game da yadda za a magance wadannan matsalolin a muhawarar da BBC ta shirya.
Dan takarar jam'iyyar Accord, Pade Okunọla, shi ma ya kada kuri'arsa.
Wani jami'in masu sa ido a zabe na tarayyar Turai ya ce saya da sayarwan kuri'u ba abu mai kyau bane. A lokacin da yake zantawa da manema labarai, jami'in ya ce alamu sun nuna cewar hukumar zaben Najeriya, INEC, ta samu cigaba game da yadda take gudanar da zabe a zaben gwamnan a jihar Osun din.
Mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya, Yusuf Lasun, ya kada kuri'arsa
Ana cigaba da zabe a mazabar Babanla Gate na garin Ede.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyu da take zargi da laifin sayen kuri'u a zaben gwamnan da ake yi a jihar Osun.
A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ta ce tana kan zafafa bincikenta game da lamarin.
Dan takarar jam'iyyar SDP, Iyiola Omisore, ya kada kuri'arsa a Ile-Ife
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta fara bincike bisa zargin da PDP ta yi cewar jami'an jam'iyyar APC suna raba kudi a wata rumfar zabe.
Rundunar ta fadi haka ne a wani sakon Twitter da ta wallafa a shafinta karkashin zargin da jam'iyyar ta PDP ta yi.