Kundin tsarin mulki ya halasta sake zaben Osun - Masana

Masana shari'a a Najeriya sun ce kundin tsarin mulki ya bai wa hukumar zaben INEC damar sake zaben gwamna da aka yi a jihar Osun a ranar Asabar.

Hukumar zabe ta INEC ta ce sai an sake zabe a wasu mazabu kafin a ayyana wanda ya ci zaben gwamnan jihar Osun.

Wani lauya mai suna Muhammad Shu'aib, ya ce kundin tsarin mulki karkashin sashe na 179 karamin sashe na biyu, karkashin sadara ta farko (A) da ta biyu wato (B), ya bai wa hukumar zabe damar sake zabe a wasu mazabun.

Idan aka yi la'akari da sama da kuri'a 3000 ake bukatar sake kadawa a wasu mazabu, ko dai saboda na'urar tantance musu zabe ba ta yi aiki ba, ko kuma an tafka magudi a wasu rumfunan zabe ko kuma wurin da kwata-kwata ba a gudanar da zaben ba.

Da yake jawabi game da sakamakon zaben, babban jami'in hukumar zabe ta INEC a jihar, Farfesa Adeola Fuwape, ya ce ratar da ke tsakanin 'yan takarar da ke kan gaba a zaben gwamnan kuri'u 353 ne kawai.

Yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Nurudden Adeleke, yake da kuri'u 254, 698, shi kuwa dan takarar jam'iyyar APC Gboyega Oyetola, yana da kuri'u 254,345 ne.

Sai dai kuma an soke kuri'u 3,498 a wasu mazabu cikin wasu kananan hukumomi a zaben da aka gudanar a jihar.

An soke kuri'un wadannan mazabun ne sakamakon kwace akwatin zabe da kuma tserewar jami'in hukumar INEC.

Ganin cewar adadin kuri'un da aka soke ya fi ratar da ke tsakanin 'yan takarar da ke kan gaba, jami'in na INEC ya ce sai an sake zaben gwamna a mazabun da aka soke zabe.

Lamarin dai ya auku ne a kananan hukumomi hudu da suka hada da Orolu da Ife South da Ife North da kuma Osogbo, in ji wata sanarwar da hukumar INEC ta fitar daga baya.

Sanarwar da kwamishinan watsa labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Solomon Adedeji Soyebi, ya saka wa hannu, ta ce za a sake zaben ne a rumfunar zabe bakwai.

Zaben, da hukumar ta shirya sake yi ranar Alhamis 27 ga watan Satumba, zai bai wa mutum 3,498 da aka soke kuri'unsu damar sake kada kuri'a.