Guguwar Mangkhut ta tagayyara China

Asalin hoton, Getty Images
Mahaukaciyar guguwar da ake yi wa lakabi da Mangkhut ta mamaye lardin da ya fi yawan mutane na kasar China, inda iska mai karfi ke gudun mita 100 cikin sa'a daya.
An sanya lardin Guangdong a cikin shirin ko-ta-kwana mafi girma saboda aukuwar guguwar, wacce tuni ta afka wa Hong Kong, inda ta rusa gine-gine mafiya tsawo.
Mutanen da suka mutu a Philippines sanadin mahaukaciyar guguwar sun kama daga 30 zuwa 49 - akasarin su sun mutu ne sakamakon zaftarewar kasar da ruwan sama ya haddasa.
Ana kallon Mangkhut a matsayin guguwa mafi karfi da ta faru a shekarar 2018.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce guguwar ta yi tsanani a yankunan gabar teku da ke kusa da birnin Jiangmen ranar Lahadi da rana.
An kwashe dubban mutane daga Guangdong, kuma hukumomin yankin sun sanya dokar ko-ta-kwana mafi tsanani.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA







