An zargi Trump da bai wa 'karuwai' toshiyar baki

Mr Trump departing Washington for West Virginia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump bai ce uffan ba har yanzu

Tsohon lauyan shugaban Amurka Donald Trump, Michael Cohen, ya amsa laifin karya dokokin tara kudin yakin neman zabe lokacin da ya gurfana a wata kotun birnin New York.

Ya ce ya karya dokokin ne bisa umarnin "dan takara", ko da yake bai ambaci sunansa ba, da nufin yin tasiri a kan zaben.

Tsohon lauyan shugaban kasar ya amsa laifin ne bayan da aka yi zargin Mr Trump da ba da umarni a ba da toshiyar baki ga wasu mata da aka yi zargin karuwansa ne.

Mr Trump bai ce komai ba har yanzu kan wannan batu. Sai dai a watan Mayu ya amince cewa ya biya Cohen kudin da ya ranta masa domin bai wa matan, ko da yake kafin wancan lokacin ya musanta zargin.

Mr Cohen, mai shekara 51, ya amince da aikata laifuka takwas ranar Talata, cikin su har da zamba wurin biyan haraji da kuma ta banki, ko da yake amincewar da ya ta aikata laifi ka iya sanya wa a rage daurinda za a yi masa daga shekara 65 zuwa shekara biyar da wata uku.

A gefe daya kuma, alkalin wata kotun Alexandria da ke Virginia, ya samu tsohon shugaban kwamitin yakin neman zaben Trump Paul Manafort da laifin zamba da kaucewa biyan haraji.

Ana ganin wadannan abubuwa da suka samu Cohen da Manafort tamkar wata sharar fage ce wurin gurfanar da Mr Trump a gaban kuliya.

From left: Michael Cohen, Donald Trump, Stormy Daniels and Karen McDougal (composite image)

Asalin hoton, Getty Images