Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu 'ya san Buhari bai iya mulki ba'
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ce tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu ya san cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na tafka kura-kurai amma ya yi shiru.
Mr Saraki ya bayyana haka ne a wani martani da ya yi wa Mr Tinubu, wanda ya zargi Sanata Saraki da fcewa daga jam'iyyar APC saboda bukatu na kashin kansa.
"Na sha ganawa da Tinubu lokacin da yake jagorantar kwamitin sulhu na APC inda na yi masa korafi kan wa. Zan iya tunawa cewa a ko da yaushe shi da kansa yana korafi kan salon tafiyar da mulkin gwamnatin nan. Ya ce shi kan sa gwamnatin da ya yi fafutikar ganin ta ci zabe ba ta mutunta shi.
"Sai dai ya bayyana cewa gwara ya zabi Buhari har zuwa 2023 ko da yana gadon asibiti ne saboda idan mulki ya koma yankin kudu maso yamma shi ne zai yi takara."
Shugaban majalisar dattawan ya ce tsohon gwamnan jihar ta Legas ba zai taba yafe masa ba domin shi ne ya yi ruwa da tsaki wurin ganin APC ba ta ba shi damar zama wanda zai tsaya tara da Buhari a matsayin mataimaki ba gabanin zaben 2015.
A cewarsa, ya dauki matakin ne domin yana ganin ya kamata a samu Kirista domin gwama shi da Buhari ta yadda ba za a ce dukka Musulmai ne suka tsaya a matsayin shugaba da mataimaki ba.