Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Gobarar California za ta ci gaba da ci har karshen wata'
Jami'ai a ranar Talata sun ce ana sa rai gobarar daji mafi muni da ke addabar jihar California da ke kasar Amurka za ta ci gaba da ci har zuwa karshen watan Agusta.
Tuni dai gobarar ta lakume filin da ya kai girman eka 290,692.
Sashin kula da dazuka da kariya daga wuta ya ce yanzu haka akwai wuraren da aka kange wutar daga bazuwa.
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe bakunan wuta 18 da ke ci, yayin da ake fama da iska mai karfi.
A ranar Litini aka ayyana wutar a matsayin mafi muni a tarihin jihar ta California.
A baya dai masu aikin kashe gobara sun yi hasashen cewa za su iya kawo karshen wutar dajin zuwa tsakiyan watan Agusta, amma yanzu sun ce abin zai kai su har farkon watan Satunba.
Akalla 'yan kwana-kwana 14,000 suke aikin kashe wutar dajin.
Har yanzu dai ba a san sanadiyyar tashin wutar ba.
Amma wani kaulin na cewa sacewar tayar wata mota ce ya haifar da wutar.
Bayanin ya nuna cewa gare-garen tayar wata mota da ya rinka gurzar kwalta a ranar 23 ga watan Yuli ne sanadiyyar tashin wutar.