Gobara ta hallaka mutane da dama a kasuwar Nairobi

Akalla mutum 15 ne suka hallaka a gobarar da ta tashi a wata kasuwa da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Mutane fiye da 50 suka ji raunuka a gobarar da ta fara da tsakar daren Alhamis wadda ta janyo asarar dukiyoyi da dama.

Kasuwar ta Gikomba tana daya daga cikin kasuwannin mafiya girma da ke birnin kuma a mafiya yawan lokuta ana samun barkewar gobara, abin da ya sa ake rade-radin cewa watakila wani ne ya ta da gobarar a cewar jaridar The Standard.

Sai dai har yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

Ma'aikatan asibiti sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare wato karfe 11:30 na agogon GMT. Kuma ta bazu zuwa wasu gidaje da shaguna kafin aka iya shawo kanta.

Wasu daga cikin mutane da lamarin ya rutsa da su sun kone yayin da wasu sun shaki hayaki mai guba lokacin da suka yi kokarin kwashe kayansu.

Jami'an asibiti sun ce akwai yara hudu a cikin wadanda suka hallaka.

Hotunan kamfanin dillancin labarai na Reuters sun nuna mutane na tona abubuwan da suka rage daga cikin takarcen da ya kone da kuma toka.

An kai wadanda suka ji raunuka zuwa wasu asibitoci da ke birnin.

Kasuwar wuri ne da ake sayar da kayan gwanjo da takalma da kuma kayan lambu.

Har ila yau akwai bangaren sayar da katako wanda gobarar ta lalata.