Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukuncin kotu: Shin Bukola Saraki ya sha ke nan?
A ranar Juma'a ne Kotun Kolin Najeriya ta zartar da wani hukunci da ake ganin zai yi babban tasiri a fagen siyasar kasar, inda ta wanke shugaban majalisar tattawa daga tuhume-tuhume 18 na zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka lokacin yana gwamnan Kwara.
Sanata Bukola Saraki ya dade yana tuhumar da cewa siyasa ce kawai, kuma an shigar da ita ne saboda ya zama shugaban majalisa ba tare da son wasu jiga-jigai a kasar ba.
A watan Satumban 2015 ne gwamnatin Najeriya ta shigar da karar Saraki kan tuhume-tuhume 18 na yin karya wajen bayyana abin da ya mallaka.
Kuma tun lokacin yake zuwa kotu tare da gudanar da aikin jagorantar majalisar. Haka kuma sunan Sanata Saraki ya sha futa a wasu lamura masu sarkakiya.
A yanzu da ya samu nasara kan gwamnatin da ta ce yaki da cin hanci na daga cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba, tambayar da wasu ke yi shi ne wanne tasiri hakan zai iya yi a fagen siyasar kasar, kuma ko hakan na nufin Saraki ya sha kenan?
Nasara
Wannan na iya zama babbar nasara ga tsohon gwamnnan na Kwara a siyasance, domin ana ganin yanzu ya samu sa'ida daga dabaibayin da aka yi ma sa a fagen siyasa.
Dambarwar siyasar APC ta samo asali ne tun bayan rantsar da Saraki a matsayin shugaban majalisar dattijai.
Tun farko dai Saraki ba shi ne zabin uwar jam'iyyar ba a matsayin shugaban majalisar dattijai amma gogaggen dan siyasar ya samu nasarar darewa kan kujerar tare da taimakon wasu sanatocin APC da suka bijere da kuma wasu sanatocin PDP mai adawa.
A sanarwar da ya fitar bayan wanke shi da kotun ta yi, Saraki ya ce an kai shi kotu ne domin "cimma bukatar wasu mutane wadanda ba su ji dadin zamowarsa shugaban majalisar dattawan ba".
Zaben 2019
A baya sau biyu Saraki yana yunkurin neman tsayawa takarar shugabancin kasa a Najeriya, kuma yanzu wasu na ganin wata dama ce ga tsohon gwamnan na Kwara.
Shari'ar da yake fuskanta ce wasu ke ganin ta hana shi yin motsi tare da taka masa burki ga wasu bukatunsa na siyasa.
Ana ganin Saraki ya daga wa Buhari kafa ne tun shigowarsa jam'iyyar APC da nufin tsayawa takarar shugaban kasa.
Kuma takun-sakar da aka jima ana yi tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, ya sa wasu na yi wa Saraki kallon yana hararar kujerar Shugaba Buhari a zaben 2019, batun da ya sha musantawa, yana mai cewa lokacin yakin neman zabe bai yi ba.
Saraki dai yana cikin wadanda suka karya PDP bayan sun balle kuma suka kulla kawance da APC wanda ya kai ta ga nasarar lashe zaben 2015.
Yanzu kuma goyon bayan da Saraki yake da shi a tsakanin 'yan majalisun kasar na APC da kuma PDP, zai kara ma shi girma a siyasance da karfin fada aji kafin zaben 2019 musamman bayan hukuncin kotun.
Yadda shari'ar ta gudana
- Yunin 2017: Kotun da'ar ma'aikata ta fara yin watsi da tuhume-tuhume 18 da ake wa Saraki
- Sai gwamnatin tarayya ta daukaka kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja
- Disambar 2017: Kotun daukaka kara ta dawo da tuhume-tuhume uku cikin 18 da ake masa kuma ta umarce shi da ya koma kotun da'ar ma'aikata don ya sake kare kansa
- Daga nan ne sai Saraki ya daukaka kara zuwa kotun kolin don kalubalantar hukuncin
- 6 ga Yunin 2018: Kotun Koli ta yi watsi da dukkan tuhume-tuhume 18 da aka yi masa.
Kalubale
Duk da kotun koli ta wanke Saraki daga zargin kin bayyana kadarorin da ya mallaka, amma akwai binciken 'yan sanda da yake fuskanta.
A watan Yuni ne 'yan sandan Najeriya suka gayyaci Sanata Bukola Saraki domin ya amsa tambayoyi game da wani bincike da suke gudanarwa kan fashi da makami a jihar Kwara.
'Yan sandan sun ce wasu mutane da ake tuhuma 'yan fashi da makami da suka kama sun ambaci cewa "Saraki ne ya ke daukar nauyinsu", zargin da shugaban majalisar dattijan ya musanta, yana mai cewa "bata masa suna kawai ake son yi".
Wasu na ganin tsugune ba ta kare wa Sanata Bukola Saraki ba musamman ta la'akari da sakamakon binciken da 'yan sanda za su fito da shi.
Bayanan Panama da Paradise
Wasu na ganin ana iya tayar da bincike kan sunan Saraki da na iyalinsa da aka ambato a bayanan da aka kwarmata na Panama da kuma Paradise (papers) a 2015 da 2017.
Sanata Bukola Saraki, yana cikin jerin sunayen attajiran da aka ambato a bayanan Paradise Papers wadanda aka ce sun boye kadarori a Tsibirin Cayman Islands domin kaucewa biyan haraji.
Binciken na musamman da wasu 'yan jarida suka gudanar, sun kwarmato cewa Bukola Saraki yana da wani kamfani da ya kafa mai suna Tenia Limited a tsibirin Cayman Islands a shekarar 2001.
Sannan an ambaci sunan matarsa a bayanan Panama inda aka yi zargin ta yi rijistar wani kamfani a kasar waje domin sayen gida a birnin Landon.
Ko da yake Saraki ya kare kansa inda ya ce kamfaninsa da aka ambato bai taba aiki ba tun da aka kafa shi.
Haka kuma game da iyalinsa da aka ambato a bayanan Panama, ya taba shaida wa BBC cewa: "Ba wai kamfani ne da muka kafa da kanmu ba, a'a, lauyoyi ne suka kafa, kuma a iya saninmu babu wata doka da aka keta".
Kawo yanzu za a iya cewa Sanata Saraki ya sha bayan wannan hukunci na kotun koli, amma lokaci ne kawai zai iya tabbatar da abin da zai faru a nan gaba.