Yadda labaran karya ke ruruta rikicin makiyaya da manoma

Hotunan karya da ake yadawa a kafafan sada zumunta wanda mutane ke ikirarin rikici ne a tsakanin al'umma, na kara haifar da zaman dar-dar a Najeriya.

Hakan na faru ne kwana uku da barkewar wani mummunan rikici tsakanin wasu da ake zargin makiyaya ne da kuma manoma, lamarin da haifar da asarar rayukan mutane fiye da 200 a jihar Filato.

Wani hoton wata mata kwance a cikin ruwa face-face da jini ga kuma kafada a balle da aka wallafa a kafafan sada zumunta ana cewa wasu daga cikin hotunan rikicin ne, ya ja hankulan masu bibiyar shafin, musamman shafin twitter inda mutane fiye da 100 suka mayar da martaninsu a kai.

Kazalika wani hoto da shi ma aka rinka yada shi a shafukan sada zumuntar inda aka nuna gawar daruruwan mutane a kwance wadanda aka ce an kashe su ne sakamakon rikicin, sai dai kuma ainihin hotun ba na Najeriya ba ne, gawarwakin wasu mutane ne da suka mutu sakamakon hadarin mota a Jamhuriyar Dominican a shekarar 2015.

Dukkanin hotunan dai ba su da dadin gani, shi ya sa da an saka su a shafukan sada zumuntar ake samun ra'ayoyin mutane daban-daban.

Irin wadannan labaran karya ko hotunan karyar da ke rura wutar rikici a Najeriya, ba su kadai ba ne, domin kuwa a farkon makon da rikicin ya faru, wani babban kamfanin jarida a kasar, ya wallafa wani labari inda ya ambato cewa shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, Danladi Circoma, ya ce hare-haren da aka kai a jihar Filato, ramuwar gayya ce a kan asarar shanu 300 da 'ya'yan kungiyar ta su suka yi.

Jaridar ta ambato shugaban kungiyar Fulani makiyayan na cewa "Tun da har yanzu ba a kai ga gano shanun ba, to babu wanda zai zaci zai kwana lafiya a yankin".

Wadannan kalaman da jaridar ta ce ya yi, sun fusata mutane da dama, inda har wasu ke Allah-wadai da kalaman, amma kuma Danladi Circoman ya musanta cewa ya yi wadannan kalamai.

Hakan kuma ya sa daya daga cikin jaridun da su ka wallafa labarain ta nemi afuwa da kuma kori wakilinta da ta ce shi ne ya wallafa labarin.

Menene labaran karya?

Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Yada karya da jita-jita yanzu ba wani abu ba ne a Najeriya, musamman a kan abun da ya shafi rikicin kabilanci.

Wasu na cewa rashin samun ingantattun labarai ta kafafen sadarwa na sa masu irin wannan sana'a ta yada labaran karya samun gindin zama.

Akwai dai kimanin mutum miliyan 26 da suke amfani da shafin sada zumunta na Facebook a Najeriya, wannan dalili da kuma karuwar masu amfani da wayoyin hannu masu komai-da-ruwanka, na taimakawa wajen saurin yada jita-jita a kafafan sada zumunta.

A watan Janairun bana fadar shugaban kasa ya karyata wani labarin da aka yayata ta Twitter da ke cewa ta tabbatar da harin da makiyaya su ka kai a jihar Benue - wani abu da aka wallafa daga masu yada karya domin harzuka jama'a.

To amma an jiyo ministan watsa labarai a Najeriya na cewa yada labarin jita-jita na kara zama barazana ga kasar, sai dai ya ce gwamnati ba za ta zura ido har a yi wa kasar sakiyar da babu ruwa ba.

Karanta wasu karin labarai

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita. Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke.