Kalli bidiyon yadda aka kona motoci a rikicin Filato

Shugabannin al'umma a jihar Filato ta Najeriya sun ce sama da mutum 200 ne aka kashe a rikicin da aka yi a wasu kauyukan jihar tsakanin manoma da kuma makiyaya.

Sai dai 'yan sanda a jihar sun ce mutum 86 ne aka kashe.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin sannan ya yi kiran da aka kwantar da hankali kuma a zauna da juna lafiya.

Wannan bidiyon ya nuna yadda aka yi asarar dukiya a rikicin ba ya ga rayuka.