Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: An kashe 'mutane da dama' a rikicin kabilanci a Ebonyi
An kashe mutane da dama yayin da wasu gwammai suka salwanta a rikici tsakanin wasu kabilun jihar Ebonyi da Cross River a kudancin Najeriya.
Rikicin na baya-bayan nan wanda ya barke a ranar Alhamis da ta gabata, ya shafi kabilun Ndi a karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi da kuma kabilun Ukelle a jihar Cross Rivers.
Wasu mutanen yankin sun shaidawa wakilin BBC cewa sama da mutum 300 aka kashe a rikicin tsakanin kabilun biyu.
Bangarorin biyu na rikici ne kan filayen noma da suka yi iyaka da juna, inda kowannensu ke ikirarin shi ya mallaki filin.
Lokacin da sashin Igbo na BBC ya ziyarci yankin, ya samu cewa garin Ndi ya koma kango, ba kowa a gidaje da kasuwa da makarantu da wuraren ibada, mutane duk sun fice daga garin.
Sarkin garin Ndi da ke karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi ya shaida wa BBC cewa rikicin ya fara ne tun a shekarar 2005, lokacin da mutanen garinsa da na Ukelle a jihar Cross River suka fara ikirarin mallakar wani filin noma da ya ratsa ta cikin karamar hukumar Izzi.
Filin da ake takaddama a kansa yana da fadi, kuma akwai rafi da ya ratsa ta dajin.
Wasu daga cikin matasan da BBC ta zanta da su, sun sha alwashin yin ramuwar gayya saboda 'yan uwansu da suke zargin mutanen Ukelle ne suka kashe su.
Matasan kuma sun hana BBC ziyartar garin Nfuma, inda rahotanni suka ce an kashe gwamman mutane da kona gidaje sama da 200, saboda sun dauki duk wani bako a matsayin dan leken asiri.
Yanzu dai ana cikin hali ne na rashin tabbas a yankin, yayin da ake fargabar sake kai sabbin hare-hare tsakanin bangarorin biyu.
Sarakuna a yankin sun yi kira ga gwamnati ta gaggauta shiga tsakani ta hanyar killace filin da shata iyaka tsakanin jihar Ebonyi da jihar Cross River.