Mu ba 'yan amshin shatan Buhari ba ne - Majalisa

Majalisar dokokin Najeriya ta mayar da martani game da korafin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi a kan cewa bangaren ya yi masa cushe a cikin kasafin kudin da ya mika masa.

Shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar, Abdulrazak Namdas, ya ce daya daga cikin dalilan da suka sa majalisar ta rage kudaden da za a saka a wasu ayyuka shi ne ganin cewa ba lallai ba ne a iya amfani da kudaden da aka fitar wa ayyukan cikin shekara daya ba.

Shugaba Buhari ya ce bai ji dadin yadda 'yan majalisar suka ki neman izinin bangaren zartarwa kafin su kara wasu kudade a kasafin kudin na naira triliyan 1.9 ba, wanda ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Namdas ya ce, "Duk lokacin da aka ce majalisa ta amince da kasafin kudi, wata ranar za a ce wannan ma'aikatar an ba ta kudi kamar biliyan hudu, za ka tarar a cikin kasafin kudi.

Majalisa ba 'yan amshin shatan bangaren zartarwa ba ne, a don haka bai kamata su yi tunanin duk abin da suka turo zai wuce kamar yadda suke so ba, a cewar sanarwar.

"Amma fannin zartaswa ba zai fitar da kudin nan ba. Za ka tarar cewa har shekara ta kare bliyan daya kawai fannin zartarwa ya bayar. Za ka ga biliyan uku na zaune ba aiki.

"Mu kuma muna zaune a wannan majalisar shekara da shekaru. Ba kasafin kudin shekara daya muka gani ba, ba biyu muka gani ba, mun gan su da yawa.

"Don haka maimakon ka dauki kudi ka ajiye a wata ma'aikata wanda za a zo, a cikin biliyan 10, a sake biliyan uku ko hudu, gara ka dauki wasu kudaden da ba za a yi amfani da su ba ka kai ma'aikatar da za ta amfani jama'a," a cewar Namdas.

Game da kudin da 'yan majalisar suka kara wa kansu kuma ba tare da neman izinin bangaren zartarwa ba, dan majalisar ya ce tun shekarar 2015 ne dai ake rage wa majalisar kasafin, kuma ya ce yadda wasu ma'aikata ke neman kari haka shi ma bangaren dokoki ke namen kari.

Namdas ya kuma ce ba gaskiya ba ce cewar 'yan majalisar na yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa domin dambarwar siyasar da ake yi tsakanin bangarorin zartarwa da na dokoki, yana mai cewa wasunsu sun samu cin zabe ne da sunan shugaban na Najeriya.

Korafin Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa game da wadansu sauye-sauye da majalisa ta yi a kasafin kudin bana, bayan ya sanya hannu kansa a ranar Laraba.

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin na naira tiriliyon 9.1, bayan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a tsakiyar watan Mayu.

Sai dai shugaban ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage biliyoyin naira da aka ware don yin wadansu manyan ayyuka ba, a kasafin, wanda ya gabatar a watan Nuwambar bara.

Ayyukan sun hada da aikin tashar wutar lantarki ta Mambila da gada ta biyu ta kogin kwara da gina wadansu tituna da layin dogo da shirin gina gidaje na gwamnatin tarayya da wadansu ayyuka a bangaren kiwon lafiya da samar da tsaro da sauransu.

Sai dai 'yan majalisar sun ce sun yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da adalci a tsakanin yankunan kasar kamar yadda tsarin mulki ya ba su dama.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, ba tare da tuntubar bangaren zartarwa ba, majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14, wanda a ya sa a yanzu take da kasafin sama da naira biliyan 139 maimaikon naira biliyan 125 da aka ware mata tun da fari.

Shugaban kasar dai ya ce yana da aniyar gyara wasu muhimman sauye-sauyen da aka yi ta hanyar gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafi ga majalisar ko kuma yin gyara ga wannan kasafin.

Sharhi, Muhammad Kabir Muhammad, BBC Abuja

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta Najeriya (wato National Bureau of Statistics ko NBS a takaice) ta fitar sun nuna cewa a watan Maris, kimar hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabrairu, daga kashi 14.33 cikin 100 zuwa kashi 13.34 cikin 100.

Wannan ne kuma wata na 14 a jere da kimar hauhawar ke raguwa.

"Wannan raguwar, a karo na 14 a jere tun daga watan Janairun 2017, ta nuna hauhawar ta ragu da kashi 0.99 cikin dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana", in ji NBS.

Daga watan Fabrairun 2016 ne dai kimar hauhawar ta fara tashin gwauron zabi (lokacin da ta tashi daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu zuwa kashi 11.38 cikin dari) har ta kai matakin da aka yi shekara shida ba a kai makamancinsa ba a watan Janairun 2017, lokacin da ta kai kashi 18.72 cikin 100 (duba hoton da ke kasa).

Tattalin arzikin Najeriya a shekara uku da suka wuce

  • Mayu 2015: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
  • Fabrairu 2016: Farashin danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da $35 daga $115 a watan Yunin 2014
  • Fabrairu 2016: Kimar hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 11.38 cikin dari daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu
  • Afrilu 2016: A rubu'i na farko na 2016 kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi asarar sama da tiriliyan daya na Naira. Zuwa karshen shekarar kuma jimillar abin da ta yi asara ya tashi naira biliyan 604.
  • Yuni 2016: CBN ya karyar da darajar Naira
  • Agusta 2016: Tattalin Arzikin Najeriya ya durkushe a hukumance
  • Satumba 2017: Tattalin arzikin Najeriya ya farfado

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi ko wacce arzikin danyen mai a Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka fi arzikin man a duniya. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne matuka a kan man, ko da yake gwamnati mai ci na ikirarin fadada hanyoyin samun kudaden shigar.

A bara ne kasar ta farfado daga matsin tattalin arziki, wanda aka kwashe kimanin shekaru 25 ba ta shiga irinsa, a sanadiyyar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Danyen mai na Bonny Light wanda Najeriya ke samarwa na daga cikin mai mafi tsada a kasuwannin duniya.