APC ta sha kaye a hannun PDP a zaben jihar Oyo

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sha kaye a hannun jam'iyyar adawa ta PDP a zaben da aka yi na cike gurbi na dan majalisar dokokin Ibarapa East, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar.

A ranar Asabar ne hukumar zabe ta kasar INEC, ta ayyana Debo Ogundoyin na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'a 6,277, inda abokin karawarsa Olukunle Adeyemo na APC ya samu kuri'a 4,619.

A wata sanarwa da PDP ta fitar ta ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa ta kama hanyar samun nasara a yankin kudu maso yamma a zaben 2019 da ke zuwa.

Wasu na ganin wannan nasarar za ta kara wa PDP karfin gwiwa sannan kuma wata alama ce da ke nuna APC na bukatar yin karatun ta-nutsu.

Jam'iyyar ta APC na fama da rikice-rikice a sassa daban daban na kasar, wanda wasu ke ganin zai iya yi mata illa a zabuka masu zuwa.

An gudanar da zaben ne a rumfunan zabe 140 a mazabu 10 da ke mazabar ta Ibarapa East.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar ta sanya tsaro sosai a yankin da aka gudanar da zaben.

NAN ya kuma ce an kai kayan zabe da kuma jami'an tsaro da wuri, sannan an fara tantance mutane da kada kuri'a a kan lokaci.