Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PDP ta zargi APC da 'murkushe abokan hamayyar siyasa'
Jam'iyyar PDP da ke adawa a Najeriya ta zargi gwamnatin APC da yunkurin murkushe abokan hamayyar siyasa saboda zaben 2019.
A cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, PDP ta zargi gwamnatin Tarayya da yin bita da kullin siyasa ga 'yan adawa.
Ta kuma ce matakin ya shafi karya duk wani wanda ya ki goyon bayan takarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
BBC ta yi kokarin tuntubar bangaren APC game da zargin amma kakakin jam'iyyar Bolaji Abdullahi bai amsa kira ba.
A cikin sanarwarta, PDP ta ce shugabanta Uche Secondus na samun sakwanin barazana ga rayuwarsa tun lokacin da jam'iyyar ta aika kokenta ga Majalisar Dinkin Duniya da ke dauke da bayani kan barazanar APC ga ci gaban dimokuradiyar Najeriya.
Sanarwar ta fadi cewa, "PDP tana son 'yan Najeriya da al'ummar duniya su san wadanda za a kama da laifi idan har shugabanninta da wasu 'yan adawa suka samu kansu a yanayi na kisa da mummunan hatsari da fashi da makami ko kuma suka yi batan-dabo.
Sannan PDP ta zargi gwamnatin APC da murkushe 'yan adawa ta hanyar zarginsu da cin amanar kasa, baya ga amfani da yaki da rashawa domin karya su.
Daga karshe, PDP ta ce APC ta sa ma ta ido ne saboda ganin yadda farin jininta ya farfado tsakanin 'yan Najeriya, a matsayin wani mataki da zai yi tasiri ga samun nasararta a zaben 2019.