Nigeria ta fara daukar mataki a filayen jirgen sama kan Ebola

Za a tsawwala matakai ne domin kariya daga yaduwar Ebola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a tsawwala matakai ne domin kariya daga yaduwar Ebola

Hukumomi a Najeiya, sun ce sun dauki tsauraran matakan kariya daga bazuwar cutar Ebola a filayen jiragen sama na kasar, ta hanyar gyara naurorin auna dumin jikin fasinjoji.

Jami'an kula da filayen jirage na kasar, sun dauki wannan mataki ne tun bayan samun bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya ta ce, mutane 45 ne suka kamu, inda 25 suka mutu sanadiyyar cutar a kasar ta Congo.

Mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, ta ce an farfado da na'urori masu auna zafin jikin dan'adam a dakin isowar baki na filayen jiragen saman kasar, wadanda aka girka tun a lokacin baya da aka samu bullar cutar a kasar.

Na'urar za ta yi kara domin ankarar da jami'ai da zarar dumin jikin mutumin da ke wucewa ta karkashinta ya zarta 38 a ma'aunin yanayin zafi.

Ta kuma ce akwai asibitoci da aka tanada a filayen saukar jiragen saman wadanda za su bincika domin tantance lafiyar duk wani mutum da dumin jikinsa ya zarta yadda aka kayyade.

Kasar Najeriya dai na iyaka ne da Kamaru, wadda ita kuma ke iyaka da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda aka gano bullar cutar ta Ebola.

A wannan karo dai, har yanzu ba a gano wani da ya kamu da cutar ta Ebola a Najeriya ba.

Sannan babu jirgi da ke tashi kai-tsaye daga Najeriya zuwa kasar ta Congo.

Manyan filayen jiragen saman kasar ta Najeriya da aka sanya wa irin wadannan na'urori na auna dumin jikin dan'adam, sun hada da na Legas, da Abuja, da Kano, da Enugu, da kuma na Fatakwal.