India da Pakistan na fada a kan kasafin ruwa

Narendra Modi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Narendra Modi

Firaministan India Narendra Modi, ya kaddamar da fara aikin cibiyar samar da wutar lantarki da ke kan wata madatsar ruwa mai cike da rudani.

Pakistan dai na adawa da aikin madatsar ruwar ta India, kasancewar tashar samar da wutar lantarkin an yi ta ne kan wani rafi da ya ratsa kasashen biyu, inda Pakistan ke fargabar cewa ruwan da ke kwararowa zuwa cikin ta zai ragu.

Akwai rafuka da dama wadanda suka taso daga yanki mai tsananin sanyi na India suka ratsa ta lardin Punjab mai yawan al'umma a kasar Pakistan.

A Pakistan, rayuka da dama sun dogara ne kan wadannan rafuka, domin kashi 80 cikin 100 na amfanin gona da ake samarwa a kasar, sun dogara ne kan wadannan rafuka da suka fito daga makwaftan kasashe.

Sai dai India ta fara gina madatsun ruwa kan wadannan rafuka, inda ta ce tana bukatar samar da tashoshin samar da wutar lantarki domin cike gibin karfin wutar lantarki da take bukata.

Pakistan dai ta kai karar India a gaban kotun laifuka ta duniya, sai dai hukuncin da kotun ta yanke a shekarar 2013, ya nuna goyon baya ne ga India.

Har yanzu dai akwai yarjejeniyar kasafta ruwan wadannan rafuka da kasashen biyu suka sanya wa hannu tun shekarar 1960, sai dai al'ummar Pakistan na ci gaba da fargabar cewa, India za ta iya amfani da wadannan rafuka a matsayin makami a wani lokaci nan gaba.