Yadda aka cashe a bikin Sonam Kapoor

A ranar Lahadi 7 ga watan Mayun 2018, ne aka fara bikin 'yar Sonam, inda aka yi sakun lalle wato 'Mehindi'.

A wannan rana amarya da ango da iyayensu kai har ma da 'yan uwa da abokan arziki an yi shigar kece raini, kuma da yawa daga cikin jaruman fina-finan Indiya sun halarci sakun lallan.

An yi wa amarya lalle mai kyau, haka kawayenta ma da sauran 'yan uwanta mata duk an yi musu lallai, baya ga cashewa da aka yi a wajen, ga kuma kwalam da makulashe da aka ci a wajen.

Iyayen Sonam, wato Anil Kapoor da Sunita Kapoor, baki har kunne tun da aka fara wannan biki, haka sauran 'yan uwanta ma.

An dai yi shagalin bikin ne a gidan mahaifinta Anil Kapoor da ke Juhu a Mumbai.

Baban Amarya da dan uwan amarya wato Arjun Kapoor, sun cashe a wannan ranar sakun lallen, haka ita ma amarya ba a barta a baya ba, domin ta shiga fili duk da lallen da ke hannunta an cashe da ita.

A washegari kuma wato Talata 8 ga watan Mayun 2018, aka daura aure.

Manyan mutane baya ga jaruman fina-finan Indiya sun halarci wajen daura auren da ma bikin baki daya.

Bayan daura aure kuma, daga bisani wato da yammacin ranar, an yi kasaitacciyar walima, inda kusan duk jaruman Indiya sun halarta.

Mahifin amarya, Anil Kapoor ya cashe sosai a wannan wajen walimar, domin rawar da ya yi, ango da amaryar ma ba su yi ba, saboda tsabar farin ciki.

Anil Kapoor ya yi rawa da mutane da dama a wajen walimar, kamar shi da Shahrukh Khan da Salma Khan da Ranveer Singh da Arjun Kapoor da Varun Dhawan da Karan Johar, sun fi kowa cashewa a wajen walima.

Hotunan bikin Sonam Kapoor