Wa zai maye gurbin Ahmad S. Nuhu a sabon fim din Mujadala?

Ahmad S Nuhu

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, A shekarar 2007 ne Ahmad S Nuhu ya rasu a wani mummunan hadarin mota
Lokacin karatu: Minti 1

Shirye-shirye sun yi nisa domin sake shirya fim din Mujadala, wanda aka fara yi shekara 18 da ta gabata, kamar yadda kamfanin da ke shirya fim din ya bayyana.

Kamfanin Mai Shadda Investment ya ce za a fara nadar shirin a ranar 10 ga watan Mayu.

Jarumi Umar M Shareef shi ne zai maye gurbin marigayi Ahmad S. Nuhu, wanda shi ne ya fito a matsayin jarumi a fim din na asali.

Fim din Mujadala ya shahara sosai a tsakanin ma'abota fina-finan Hausa.

Fitaccen jarumi kuma mai shirya fim Ali Nuhu, wanda dan uwa ne ga Ahmad S. Nuhu, shi ne zai tsara fim din da kuma bada umarni.

Marigayi Ahmad S. Nuhu ya mutu ne a farkon shekara ta 2007 bayan wani mummunan hadarin mota da ya yi a hanyar Azare zuwa Maiduguri.

Mutuwarsa ta tayar da hankalin masu ruwa da tsaki a Kannywood da kuma magoya baya.

Ya kasance jarumi mai tashe da farin jini, wanda kuma aka ce abokan aikinsa na jin dadin hulda da shi.

Kamfanin Mai Shadda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa Mujadala shiri ne wanda har yanzu 'yan kallo "suna daukin gani bayan shekara kusan 18 da fitowarsa".

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram