Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tsokacin kan maganar da ya yi akan matasa wadda ta janyo ce-ce-kuce kwanakin baya.
Da ya ke magana da Sashen Hausa na VOA a lokacin da ya kai ziyara Amurka, shugaban ya ce ba a bayyana maganar tasa yadda take ba.
Shugaban ya kuma yi karin haske kan maganar da ta janyo masa suka a shafukan sada zumunta, inda ya ce matasa da dama "ba su yi makaranta ba, kuma suna son ababen more rayuwa kyauta".
Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara a kasar, abin da ya sa jami'an gwamnati daban daban suka rinka yin kokarin yin karin haske kan kalaman shugaban.
A lokacin da yake magana a wajen taron kasashe rainon Ingila ne shugaban ya yi wannan maganar inda ya ce:
"Da damansu ba su suyi makaranta ba, sannan suna cewa ai Najeriya kasa ce mai albarkar mai, don haka suna zaune ba sa komai suna jira gwamnati ta samar musu ilimi, da gida, da kula da lafiya kyauta".
Ya ce: "Toh ka san Najeriya an ce mun kai miliyan 180 ko kuma miliyan maitan.
"Kuma kashi 60 bisa 100 na su duk matasa ne, wato shekara 30 abin da ya yi kasa, mu kamar a Arewa ba su yiu makaranta ba, koko suna yi sun fita.
"Toh, baya ga dai Allah Ya sa damunan bara da ta bana ta yi albarka, yawancin su ba su da aikin yi. Suna zaune.
"Irinsu ko sun je kamar misali kudu, abin da za su samu bai ma isa su biya kudin gidan haya ba, balle abin da za su ci su sha su yi sutura ko kuma su koma gida."
Ya ce miliyoyin matasa ne suka samu aikin yi ta hanyar noma, amma 'yan jarida ba su bayyana wannan ba.
Shugaba Buhari ya kara da cewa : "Su kuma dama 'yan jarida na Najeriya balle na rubutawa a... kusan abin da suka ga dama suke yi.
"Yanzu kamar nasara da aka ci a noma da bara da bana, miliyoyin mutane sun je gona, sun yi aiki kuma abin ya yi albarka. Amma ka ga ba'a maganar. Miliyoyi! sai kullum a tashi ana zage-zage."
Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:
- Shekararsa 72
- An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
- Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
- An hambare shi a juyin mulki
- Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
- An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
- Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
- Musulmi ne daga arewacin Najeriya
- Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa