Fitattun jaruman Indiya da suka auri junansu

1. Jaya da Amitabh Bachchan

Jaya Bachchan ta yi suna a fina-finan Indiya, a lokacin shi kuma Amita yana kokarin ganin ya samu karbuwa a fina-finan. Sun yi fina-finai da dama tare tun kafin ma su fara son junansu.

A lokacin da ake shirya fim din Zanjeer wanda suka fito tare a shekarar 1973, sai soyayya ta shiga tsakaninsu, kuma bayan fitar fim din wanda ya samu karbuwa a wancan lokaci, sai suka yi aure a wannan shekarar.

Sun haifi 'ya'ya biyu, wato Shweta Bachchan wadda ba ta yin fim da kuma Abhishek Bachchan wanda shi kuma jarumi ne a fina-finan Indiya.

Har yanzu suna tare, duk da Jaya ta fuskanci matsaloli da dama a zamansu saboda ita tana da hakuri sosai shi kuma Amita yana da tsattsauran ra'ayi.

Sannan kuma da soyayyar da ya yi tare da Rekha wadda hakan har ya kusa janyo rabuwarsu da matar tasa.

Wasu daga cikin fina-finan da suka yi tare akwai Sholay da Silsila da kuma Mili.

2. Hema Malini da Dharmendra

Dharmendra da Hema, su ma sun yi tashe sosai a fina-finan Indiya. A lokacin su, Hema na daga cikin jarumai matan da ake yayi saboda kyawunta.

Ta yi samari da dama a cikin jarumai maza ciki har da Jeetandra da Dev Anand da kuma Manoj Kumar.

A lokacin da ake shirya fim din Tum Haseen Main Jawan, wanda suka fito tare a shekarar 1970, sai suka fara soyayyar.

Dharmendra ya yi aure a lokacin, kuma gashi yana son Hema, ya nemi sakin matarsa mahaifiyar su Sunny Deol ta ki yarda, sai kawai ya ce ai Musulunci ya bayar da damar auren mace fiye da daya, don haka sai ya Musulunta kawai ya auri Hema a ranar 21 ga watan Augustan 1979.

Sun haifi 'ya'ya mata biyu wato Esha Deol wadda jaruma ce itama da kuma Ahana Deol. Har yanzu suna tare, kuma sun aurar da 'ya'yan nasu har da jikoki ma.

Fina-finan da Hema da Dhramendra suka fito tare sun hada da Jugnu da Charas da kuma Seeta aur Geeta.

3. Neetu Singh da Rishi Kapoor

Neetu Singh ta fara fim ne tun ta na karama, kamar yadda shi ma Rishi Kapoor ya fara fim din tun yana karami.

A loakcin da ake shirya fim din Kabhi Kabhi, a lokacin ne suka fahimci cewa suna son juna, saboda Rishi ba ya boyewa Neetu komai na sirrinsa, har ma da 'yan matansa, saboda shi akwai shi da son mata.

Bayan da ya yi wata doguwar tafiya ne sai ya fahimci cewa yana kewar Neetu, anan ne ya gane cewa lallai sonta ya ke, sai ya aika mata da wasika, nan take kuma ta amince da soyayyar ta sa.

Saboda ta yi karama a aurar da ita a lokacin, sai aka yi ta ya-madidi da maganar soyayyar ta su, sai da suka shafe shekara biyar suna soyayyar, sannan suka yi aure a lokacin tana shekara 21 a 1980.

Sun haifi 'ya'ya biyu wato Riddhima Kapoor da kuma Ranbir Kapoor wanda shi ma yanzu haka yana yin fim.

Har yanzu suna tare, to amma a baya sai da Neetu ta bar gidan Rishi saboda matsalarsa ta yawan shan giya. Fina-finan da suka fito tare sun hada da Khel Khel Mein da Jhoota Kahin Ka da kuma Zinda Dil.

4. Kajol da Ajay Devgan

Halayyar Kajol ta sha ban-bam da ta Ajay. Kajol mace ce mai faran-faran ga zolaya, shi kuwa Ajay bai fiye fara'a ba.

Sun fara fim tare ne a 1995 fim din Hulchul, daga nan dai suka fara dan shakuwa, saboda Kajol ta gane halayyarsa, ta san yadda take tafiyar da shi har ma ta kan sashi dariya wasu lokuta.

A shekarar 1999 ne suka yi aure bayan sun shafe shekara hudu suna soyayya.

Har yanzu suna tare ba tare da wata matsala ba, kuma sun haifi 'ya'ya biyu, Nysa Devgan wadda ba ta fi shekara 16 ba a yanzu da kuma Yug Devgan wanda bai fi shekara bakwai ba a yanzu.

Fina-finan da suka fito tare sun hadar da Ishq da Dil Kya Kare da kuma Pyar To Hoona Hi Tha.

5. Aishwarya Rai da Abhishek Bachchan

A shekarar 2006, Abhishek da Aishwarya sun fito a fina-finai uku tare wato Umrao Jaan da Guru da kuma Dhoom 2.

Kasancewar su na tare a wannan lokaci, sai suka fahimci cewa su na son juna.

A shekarar 2007 Abhishek ya nuna cewar yana son aurenta ta kuma amince, a wannan shekarar ne kuma aka daura musu aure.

Duk da Aishwarya ta girmi Abhishek da shekara biyu, su na zamansu lafiya har ma da 'yarsu guda wato Aaradhya.

6. Twinkle Khanna da Akshay Kumar

Twinkle Khanna ta ce ba ta taba jin dadin kasancewarta jaruma ba, sai da ta hadu da Akshay Kumar har su ka yi fim tare.

Duk da Akshay ya yi soyayya da wasu jarumai kamar Shilpa Shetty, daga baya sai ya koma son Twinkle.

Sun yi aure ne a 2001, kuma su na da yara biyu, wato Aarav da Nitara. Sun yi fim tare kamar Zulmi da kuma International Khiladi.

Har yanzu su na tare suna kuma zaman lafiya, ita Twinkle tuni ta ajiye fitowa a fim.

7. Kareena Kapoor da Saif Ali Khan

Kareena Kapoor jaruma ce da ta ke tashe har yanzu, haka shi ma Saif Ali Khan. Jaruman biyu sun fito tare a cikin fina-finai da dama.

Duk da Saif Ali Khan ya taba aure har ma da yaransa biyu wanda sun tasa, hakan bai hana Kareena tsunduma cikin kogin son sa ba, haka shima Saif din.

Fim din da suka yi tare na Tashan shi ne sanadin fara soyayyarsu, a lokacin Kareena ta gano cewa lallai Saif shi ne mutumin da za ta iya zama da shi a matsayin mijinta, saboda yadda ya ke kula da ita da kuma sanya ta dariya a kodayaushe.

A shekarar 2009 ne, jaruman suka fito suka bayyana soyayyarsu a fili lamarin da ya bai wa kowa mamaki. A watan Oktoban 2012 ne suka yi aure.

An yi shagalin biki sosai a lokacin. Yanzu haka sun haifi da daya wato Taimur, kuma suna zaman su lafiya.

Ko bayan aurenta, Kareena ta ci gaba da yin fim, haka shi ma mijin, kuma akwai kyakkyawar fahimta tsakanin Kareena da 'ya'yan mijinta wato Sara wadda ta ke da shekara 24 da kuma Ibrahim 17.

Tuni da ma Saif suka rabu da matarsa wadda ta girme masa sosai wato Amrita Singh, ita ma jaruma ce.

Daga cikin fina-finan da Saif da Kareena suka yi tare akwai Omkara da Agent Vinod da kuma Kurbaan.

8. Genelia da Riteish Deshmukh

Sun fara haduwa ne tun a lokacin da aka fara gwajin fim dinsu na farko wato Tujhe Meri Kasam.

Tun daga nan ne sai suka zama aminan juna. Bayan wasu shekaru kuma sai suka fahimci cewa amintarsu fa ta dace su yi aure saboda sun fahimci juna sosai.

A shekarar 2012 ne suka yi aure, kuma yanzu haka su na da yara biyu.

Sun yi fina-finai tare kamar Teere Naal Love Ho Gaya da kuma Masti.

9. Soha Ali Khan da Kunal Khemu

Soha da Kunal sun fara haduwa ne a shekarar 2009, lokacin da ake shirya fina-finan Dhoondhte Reh Jaoge da kuma 99, wanda suka fito tare.

Da farko dai ba bu wata shakuwa tsakaninsu sai ta fim, amma daga bisani sai suka fara shiri, a hankali kuma har soyayya ta shiga tsakaninsu.

Sun dauki lokaci mai tsawo suna soyayya, daga bisani kuma suka yanke shawarar aurar juna, inda aka daura musu aure a 2015.

Yanzu sun haifi 'ya mace, su na kuma zaman su lafiya.