An sace wani baturen Jamus a Nijar

Shugaba Muhammadou Issufou na Jamhuriyar Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadou Issufou na Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an sace wani Bajamushe da ke gudanar da ayukan jin-kai a kusa da iyakar Mali.

A cewar ministan shari'a kuma Antoni-Janar din kasar, 'yan bindiga a kan babura ne suka sace mutumin mai suna, Joerg Lange, a garin Inates da ke yammacin kasar.

Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan 'yan bindigar.

Sai dai mayakan jihadi da ke da alaka da al-Qaeda da Kungiyar IS, sun sha kai hare-hare a kan jami'an tsaro da fararen hula a iyakar kasar da Mali.